'Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna, Sun Kashe Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara

'Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna, Sun Kashe Sakataren Jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara

  • Yan bindiga sun harbe sakataren jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe, Musa Ille, har lahira a jihar Zamfara ranar Litinin da daddare
  • Shugaban jam'iyyar PDP na Tsafe, Garba Garewa, ne ya tabbatar da haka ranar Talata, ya ce maharan sun harbe shi a ƙofar gidansa
  • Wani mazaunin garin Tsafe ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yaudari sakataren PDP da cewa ya fito ya duba wani abu, nan take suka kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe Musa Ille, sakataren Peoples Democratic Party (PDP) a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Maharan sun kashe babban jigon PDP kuma sakatare a ƙofar gidansa lokacin da suka kai masa farmaki ranar Litinin da daddare.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki hedkwatar ƙaramar hukuma, sun tafka ɓarna

Gwamna Dauda Lawal na PDP.
Sakataren PDP na Tsafe a Zamfara ya rasa ransa a hannun ƴan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe, Garba Garewa, shi ne ya tabbatar da kisan sakataren ga Channels tv ranar Talata, 16 ga watan Aprilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna zargin wadanda suka kashe shi 'yan bindigan daji ne, sun shiga gidansa jiya (Litinin) suka harbe shi har lahira," in ji Garewa.

Yadda aka kashe sakataren PDP

Wani mazaunin yankin, Abubakar Tsafe, ya shaidawa gidan talabijin cewa a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga unguwar, sai suka kira sakataren ya zo ya duba wani abu a bayan gidansa.

A cewarsa, Musa Ille ya fito waje domin dubawa kamar yadda suka nema ba tare da sanin su ‘yan fashin daji ba ne dauke da mugayen makamai.

Har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton rundunar ƴan sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamarin ba, cewar The Cable.

Kara karanta wannan

Za a ja daga tsakanin Wike da Atiku kan shugabancin jam'iyyar PDP

Mazauna Tsafe sun koka

Haka nan wani ɗan asalin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Legit Hausa cewa a ƴan kwanakin nan ƴan bindiga sun matsawa mutane a Tsafe da kewaye.

Ya ce jami'an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu idan aka sanar da su amma wani lokacin abin yana fin ƙarfinsu, inda ya ƙara da addu'ar Allah ya jikan Alhaji Musa Ille Tsafe, marigayi sakataren PDP.

"Ba abin da zan ce sai Allah ya jiƙan Alhaji Musa Ille Tsafe ya kuma bi masa haƙƙinsa. A ƴan kwanakin nan ƴan bindiga sun matsa mana, Allah ya kawo mana ɗauki," in ji shi.

Ƴan ta'adda sun bakunci lahira

A wani rahoton kuma Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin ISWAP da wasu mayaƙansu a jihar Borno.

Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabwet ya ce wannan samamen ya lalata muhimman kayayyakin ƴan ta'addan a gabar tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262