Katsina: Gwamna Dikko Radda Ya Yi Muhimmin Nadi a Gwamnatinsa
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Alhaji Falalu Bawale a matsayin shugaban ma'aikata (HoS) na jihar Katsina
- Alhaji Bawale ya karbi mukamin ne daga Alhaji Usman Isyaku wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati bayan ya shafe shekaru 35 a aikin
- Ibrahim Kaula Muhammad, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar ya sanar da hakan a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Alhaji Falalu Bawale a matsayin shugaban ma'aikata (HoS) na jihar Katsina.
Bawale har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin HoS ya kasance babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikata na Katsina.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Ibrahim Kaula Muhammad, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dikko Radda ya yi wani nadin
Sanarwar wadda Isah Miqdad, mai tallafawa gwamnan ta fuskar kafofin yada labarai ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) ta ce:
"Alhaji Bawale ya karbi mukamin ne daga Alhaji Usman Isyaku wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati bayan ya shafe shekaru 35 yana aiki."
Gwamna Radda ya kuma amince da nadin tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin harkokin gwamnati.
Gwamna Radda ya taya sabon shugaban ma’aikata murnar nadin da aka yi masa, ya kuma bukace shi da ya yi amfani da kwarewa a sabon aikinsa.
Kadan daga tarihin Alhaji Bawale
An haifi Alhaji Bawale a ranar 15 ga watan Agusta, 1966 a yankin 'Yaradua, karamar hukumar Katsina.
Ya kammala karatunsa na digiri na farko shekarar 1990 a jami’ar Ahmadu Bello a fannin fasahar harsuna.
Sannan Bawale ya samu shaidar kammala PGD a fannin gudanarwa (PGDM) a kwalejin kimiyya ta Hassan Usman Katsina a shekarar 2002.
Alhaji Bawale ya wuce jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 2005 inda ya sami digiri na biyu a fannin siyasa da harkokin mulki.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Wazirin Zazzau, Hakimin Ikara ya rasu
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar Injiniya Aminu Umar, Wazirin Zazzau kuma Hakimin Ikara.
Tuni aka yi jana'izarsa kamar yadda addini ya tanadar a Zariya da ke jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng