Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Talaka Zai Amfana da Kudaden Tallafin Wutar Lantarki da Aka Cire

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Talaka Zai Amfana da Kudaden Tallafin Wutar Lantarki da Aka Cire

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da ta yi a cikin ƴan kwanakin nan
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da aka samu wajen inganta samar da wutar lantarki a ƙasar nan
  • Mohammed Idris ya yi bayanin cewa har yanzu akwai masu amfana da tallafin wutar lantarki a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

Ministan ya ce sama da Naira tiriliyan 1 da za a samu sakamakon janye tallafin wutar lantarki, za a yi amfani da su wajen inganta samar wutar lantarki da ayyukan more rayuwa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Dalilin janye tallafin lantarki
Za a yi amfani da kudaden janye tallafin lantarki wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin 'Hannu da Yawa' na Rediyo Najeriya da ke Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnati za ta yi da kuɗaɗen?

Ministan ya ce wasu ƴan tsiraru masu hannu da shuni da kamfanoni ne kawai ke kwashe garaɓasar tallafin wutar lantarkin.

A cewarsa kaso 40% na tallafin wutar lantarkin yana amfanar kaso 15% da ke samun wutar lantarki ta sa'o'i 20 a kowace rana, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

A kalamansa:

"Yana da kyau a bayyana cewa kuɗaɗen da za a samu daga janye tallafin lantarkin, za a sake sanya su ne wajen inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, da sauran abubuwa masu muhimmanci kamar ilmi da kiwon lafiya."

Idris ya jaddada cewa har yanzu kaso 85% cikin 100% na al’ummar da suke ƙarƙashin sauran rukunonin wutar lantarkin na samun tallafi.

Kara karanta wannan

'Yan daba 200 sun tuba, sun zama nagari, inji Gwamnan Kano

Wutar lantarki za ta wadata a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan makamashi Bayo Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya bayar da wutar lantarki ta sa'o'i 20 nan da shekara uku.

Gwamnatin za ta cimma wannan kudirin ne ta hanyar mayar da duka 'yan Nijeriya kan tsarin Band A, wadanda ke samun wuta sa'o'i 20 a rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng