Sabuwar Matsala Ta Kunno Kan Emefiele Bayan an Fallasa Yadda Yake Karbar Daloli a Kotu

Sabuwar Matsala Ta Kunno Kan Emefiele Bayan an Fallasa Yadda Yake Karbar Daloli a Kotu

  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya sake shiga cikin sabuwar matsala
  • Ɗan aiken Emefiele, Monday Osazuwa ya shaidawa kotun laifuffuka ta musamman da ke Legas yadda wanda ake ƙara ke aikensa ya karɓo Dala
  • Osazuwa ya ce Emefiele ya umurce shi a lokuta daban-daban da ya karɓo kuɗaɗen da suka kai Dala miliyan uku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ikeja, jihar Legas - Wani direban mota mai suna Monday Osazuwa, ya bayyana yadda ya karɓo tsabar kuɗi har Dala miliyan uku ga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.

Osazuwa ya bayyana cewa Emefiele ya umurce shi da ya karɓo kuɗaɗen a lokuta daban-daban.

An fallasa yadda Emefiele yake karbo Daloli
Godwin Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume Hoto: @thecableindex
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne yayin da lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN) ya gabatar da shi a matsayin shaida a gaban kotun manyan laifuka da ke Legas a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya faɗi watan da yan Najeriya za su fita daga ƙangin tsadar rayuwa a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shaida wa kotun cewa ya fara aiki da bankin Zenith ne a matsayin mai tuƙa kaya a shekarar 2001 yayin da Emefiele ya kasance manajan darakta na bankin.

Emefiele yana sa a 'karɓo' masa daloli

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, ya ce shi ne yake kula da takardu yayin da yake aiki a ofishin gwamnan na CBN da ke Legas.

"Zan iya tunawa, a shekarar 2020, lokacin da baya cikin Legas, Emefiele ya kira ni ya ba ni wata lamba cewa wani mutum yana da wani abu da zan karɓa daga wurinsa, kuma mutumin zai ba ni lambar wani daban."
"Lokacin da na isa ofishin mutumin, an ba ni wani ƙunshin kuɗi. Na ƙirga kuɗin da ke ciki, aka ce na ba maigida na."

Ina yake kai dalolin idan ya karɓa?

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 150, sun samu nasarori a Arewacin Najeriya

Ya kuma ƙara da cewa duk lokacin da Emefiele baya nan, yana ba wanda ake ƙara na biyu, Henry Omoile kuɗin ne bisa umurnin tsohon gwamnan na CBN.

Osazuwa ya ba da labarin yadda yake kai kuɗin zuwa gidan Emefiele da ke Iru Close, Ikoyi, Legas.

Ya shaida wa mai shari’a Raman Oshodi yayin da yake tsayawa a matsayin shaida cewa Emefiele ya kan karɓo kuɗi shi kaɗai a duk lokacin da ya ke Legas.

Kotu ta bada belin Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai shari’a Rahman Oshodi na wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja a ranar Juma’a ya bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a kan N50m.

Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume guda 26 da suka hada da zamba a ofis da kuma karkatar da dala biliyan 4.5 da kuma Naira biliyan 2.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng