Kotun Legas Ta Yi Hukunci Kan Bukatar Bayar da Belin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele
- Wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a kan N50m
- Mai shari’a Rahman Oshodi ya ce Emefiele na da bukatar mutane biyu da za su tsaya masa kuma dole su kasance masu biyan haraji ga Legas
- Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume guda 26 da suka hada da zamba a ofis da kuma karkatar da $4.5bn da kuma N2.8bn
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Mai shari’a Rahman Oshodi na wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja a ranar Juma’a ya bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a kan N50m.
Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume guda 26 da suka hada da zamba a ofis da kuma karkatar da dala biliyan 4.5 da kuma Naira biliyan 2.8, jaridar The Cable ta ruwaito.
Mai shari’a Oshodi, a hukuncin da ya yanke, ya bayar da belin Emefiele a kan Naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sharudan belin Godwin Emefiele
Oshodi ya ce dole wadanda za su tsaya wa Emefiele su kasance suna da aikin yi sannan kuma sun biya gwamnatin jihar Legas harajin shekara uku.
Jaridar The Nation ta ruwaito alkalin ya ce dole ne mutanen su nuna takardun da ta suka cika ka'ida kuma dole ne a yi musu rajista a tsarin kula da beli na jihar Legas.
Oshodi, ya ce dole ne a tura takardun belin zuwa kotun laifuffuka ta musamman sannan a yi rajista a tsarin kula da beli na jihar Legas.
Kotu ta ba da umarnin tsare Emefiele
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa babbar kotun jihar Legas ta ba da umarnin cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Wannan na zuwa bayan da EFCC ta gurfanar da Emefiele gaban kotun bisa zargin ya aikata laifuffuka 26 da suka hada da zamba a ofis da kuma karkatar da kudi.
Tun a wannan zaman kotun na ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024, lauyan Emefiele ya nemi beli tare da gabatar da hujjojinsa ga alƙali.
Asali: Legit.ng