Na ji Dadin Yadda Masu Kudi Suka Gudanar da Azumin Ramadan, Gwamnan Sokoto

Na ji Dadin Yadda Masu Kudi Suka Gudanar da Azumin Ramadan, Gwamnan Sokoto

  • Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya bayyana jin dadin yadda masu kudin cikin musulmi suka gudanar da azumin bana da ya kammala a jiya
  • Ya ce ya yi farin ciki da yadda masu halin suka dage da taimakawa mabukatan cikinsu a cikin watan azumin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na x
  • Gwamnan ya ce shi ma gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen taimakawa talakawa, inda ya nemi su dage da yiwa jihar Sokoto addu'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ce ya ji daɗin yadda masu kuɗi suka gudanar da azumin watan Ramadanan bana.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnan Arewa ya faɗi alamun da ke nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in talakawa a Ramadan

Ya faɗi hakan ne ta cikin saƙon barka da sallah da ya wallafa a shafinsa na X.

Gwamnan ya ce gwanin sha'awa yadda masu hali suka taimakawa talakawa a wajen sauƙaƙa musu halin da ake ciki.

Gwamna Ahmed Aliyu ya mika sakon barka da sallah
Gwamnan ya ce ya ji dadi sosai yadda masu hali suka taimaki mabukata Hoto:@Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Aliyu ya kara da cewa:

"Abin sha'awa ne ka ga masu kudi suna taimakawa mabukatan cikinsu. Abinda da suka yi abin a yaba ne sosai."

Gwamna Ahmad Aliyu ya ce shi ma gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen taimakawa mabuƙatan jihar, musamman cikin watan azumin Ramadan.

Ya kuma shawarci musulmi su yi riko sosai da halayen kwarai da suka dinga yi lokacin azumin domin samun jin dadin zamantakewa tsakanin al'umma.

"Ya kamata muyi wa Sokoto addu'a" - Aliyu

Gwamna Ahmed Aliyu kuma bayyana muhimmancin yin addu'a wajen samun ci gaba a jihar Sokoto, kamar yadda Tribune online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya aike da muhimmin saƙo bayan kammala ƙaramar Sallah a Najeriya

Ya ce:

"Ina kira ga kowa da kowa musamman malamai, da su yi addu'o'i wajen neman kariyar Allah. Mu zo mu yi aiki tare wajen ci gaban jihar Sokoto da bayar da shawarwari masu amfani."

Gwamnatin Sokoto ta daɗaɗawa ma'aikata da azumi

Tun cikin azumin watan Ramadan gwamnatin jihar Sokoto ta yiwa ma'aikatanta albishir da cewa za ta biya su wani kaso na albashinsu domin taimakawa wajen siyayyar azumi.

Ta biya ma'aikatan rabin albashinsu kyauta ba tare da an cire wani kaso daga kuɗin da aka biya su a ƙarshen wata ba.

.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Tags: