Azumi 30: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za a Yi Ƙaramar Sallah a Najeriya
- Fadar mai martaba Sarkin Musulmi ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Ƙaramar Sallah ba a faɗin Najeriya ranar Litinin
- Bisa haka ta bayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar da Musulmai za su yi Ƙaramar Sallah
- Hakan na nufin za a tashi da azumin ranar Talata domin cika 30 kamar yadda addinin musulunci ya tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad na III, ya ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar da za a yi Sallah Ƙarama.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal a faɗin Najeriya ranar Litinin, 29 ga watan Ramadan. 1445AH.
Sultan wanda shi ne shugaban majalisar ƙoli ta harkokin Musulunci a Najeriya ya tabbatar da haka ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata ya wallafa a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin Musulunci na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu, ta ce ba a ga watan Shawwal ba.
Ta ce fadar Sarkin Musulmi ta amince da rahotanni rashin ganin watan kuma ta ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar 1 ga watan Ƙaramar Sallah.
Sultan ya tura saƙo ga ƴan Najeriya
"Mai alfarma Sarkin Musulmi na taya ɗaukacin al'ummar Musulmai barka da Sallah tare da fatan Allah ya ƙara tabbatar da su a kan tafarkin shiriya.
"Sultan ya kuma roƙi musulmai su ci gaba da addu'ar neman zama lafiya kana ya taya su murnar zuwan idin Karamar Sallah (Eid-El-Fitri)."
- Cewar sanarwar.
Saudiyya ta fitar da sanarwa
Wannan na zuwa ne awanni bayan ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba, za a ci gaba da azumi ranar Talata.
Har ila yau, ta kara da cewa za a gudanar da Sallar Eid-El-Fitr ne a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu bayan cika azumi 30.
Sheikh Idris ya koma Bauchi
A wani rahoton kuma Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya samu tarba daga magoya bayansa, inda suka taro shi daga bayan gari har zuwa kofar gidansa.
Dalibansa sun ce malamin ya samu gagarumar nasara cikin wata hijira da ya yi ta tsawon makonni.
Asali: Legit.ng