Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi Sama Da 300 A Kano

Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi Sama Da 300 A Kano

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta samu gagarumin nasara wajen yaki da ta'ammalli da miyagun kwayoyi
  • A cikin watanni 3, ta kama mutane 319 da ake zargi suna da hannu dumu-dumu cikin harkar kwaya a Kano, 14 mata sauran 305 kuma maza ne
  • Hukumar ta kuma cafke tan 4.7 na mugayen kwayoyi, cikin su akwai tramadol, wiwi da sauran kayan gusar da hankali

Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA ya bayyana samun gagarumar nasarar kama mutane 319 da ake zargi da ta'ammalli da miyagun ƙwayoyi a sassan jihar Kano.

Leadership ta ruwaito cewa kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya ce cikin waɗanda aka kama, 14 mata ne sauran 305 kuma maza.

Hukumar NDLEA ta dakume wasu da mutum 319 bisa zargin ta'ammali da miyagun kwayoyi a Kano
Hukumar NDLEA ta kama mutanen ne a sassa daban-daban na Kano. Hoto: www.ndlea.gov.ng
Asali: UGC

Kwamandan ya kara da cewa sun kuma samu nasarar cafke tan 4.7 na muggan ƙwayoyi a tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2024.

Kara karanta wannan

Kaduna: An bayyana adadin ƴan shi'a da suka mutu a rikicin da ya faru, ƴan sanda sun yi raddi

"Jimillar ƙwayoyin da muka kama sun haura tan huɗu, ciki har da wiwi da sauran miyagun ƙwayoyi masu gusar da hankali."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Abubakar Idris Ahmad

A cikin aikin da hukumar NDLEAn ta yi, kwamandan ya ce jami'ansu sun ƙwato tramadol kimanin 1.9kg a sumamen da suka kai sassan Kano.

NDLEA na ayyukan ceto 'yan kwaya

Jami'in ya ce ayyukan da su ke yi yanzu ya wuce kawai a kama masu ta'ammalli da miyagun ƙwayoyin.

"Mun samu nasara a kotu inda aka ɗaure mutane 33 da ake zargi da ta'ammalli da miyagun ƙwayoyi a Kano."
"Mun kuma samu nasarar kai ƴan ƙwaya 26 gidan gyara tarbiyya, da yiwa mutane 30 a masarautar Kano gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi."

- Abubakar Idris Ahmad

Yayin da ake sa ran fara bukukuwan sallah a wannan makon, Abubakar Ahmad Idris ya ce za su ruɓanya ƙoƙari wajen daƙile amfani da miyagun ƙwayoyi tsakanin matasan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutane sama da 100 bisa zargin aikata wasu laifuka a jihar Kano

Mutane 198 NDLEA ta Kama a Janairu

A farkon shekarar nan ma sai da hukumar ta NDLEA ta sanar da kama wasu mutane 198 da ake zargi da hada-hadar miyagun kwayoyin.

An kama mutanen ne a wuraren hada-hadar kwayoyi kimanin 21 a sassan jihar Kano, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cikin adadin, 177 maza ne, sauran 21 kuma mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.