Emefiele: Kotu Ta Ɗauki Mataki 1 Kan Tsohon Gwamnan CBN Bayan EFCC Ta Ƙara Gurfanar da Shi

Emefiele: Kotu Ta Ɗauki Mataki 1 Kan Tsohon Gwamnan CBN Bayan EFCC Ta Ƙara Gurfanar da Shi

  • Kotu ta ba da umarnin cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya a hannunta
  • Wannan umarni na zuwa ne bayan Godwin Emefiele ya sake gurfana a gaba babbar kotun jihar Legas kan tuhume-tuhume 26
  • Lauyan Emefiele ya nemi beli a zaman kotun na ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024, ya gabatar da hujjojinsa ga alƙali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Babbar kotun jihar Legas mai zama a Ikeja ta umarci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC) ta tsare Godwin Emefiele a hannunta.

Mai shari'a Rahman Oshodi shi ne ya ba da umarnin garƙame tsohon gwamnan CBN a kurkukun EFCC bayan gurfanar da shi ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Kotu ta kora babban jami'in kamfanin Binance zuwa gidan gyaran hali

Emefiele a Kotu.
EFCC za ta riƙe Emefiele bisa umarnin babbar kotun Legas Hoto: Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, alkalin ya ɗauki wannan matakin ne kan zargin Emefiele da hannu a almundahanar $5.5bn da N2.8bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma kotun ta umarci a garƙame wanda ake tuhumarsu tare, Henry Isioma-Omoile, a gidan gyaran hali da ke Ikoyi.

Godwin Emefiele ya nemi beli

Tun da farko dai lauyan waɗanda ake ƙara, Mista A. Labi-Lawal, ya miƙa takardun neman beli guda biyu, inda ya roƙi alkalin ya ba da belin waɗanda ake ƙara saboda sanannun mutane ne.

Labi-Lawal ya ce wanda ake kara na farko (Emefiele) ya cika bukatar belin da mai shari’a Muazu ya ba shi a shari’ar da ake yi masa ta zamba a Abuja.

Ya kuma shaidawa kotun Legas cewa dukkan sababbin tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan CBN ana iya ba da beli saboda ba manyan laifuka bane.

Kara karanta wannan

Tuhuma kan aikata laifuffuka 26, Emefiele ya isa kotu, ya gurfana gaban alkali

"Ya kuma kamata kotu ta yi la’akari da matsayin wanda ake kara na farko a matsayinsa na tsohon gwamnan CBN na kasar nan,” inji shi.

Lauyan wanda ake kara ya ce wanda yake karewa ya gabatar da kansa a gaban mai shari’a Muazu a Abuja domin ya amsa tuhumar da ake masa.

A cewarsa, tsohon gwamnan CBN ba shi da wata matsala da jirgin da zai kawo shi ya halarci zaman kotun domin shi ne mutum na farko da ya fara zuwa kotu.

Emefiele da wanda ake tuhumarsu tare sun musanta dukkan laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa bayan gurfanar da su a gaban kuliya yau Litinin, The Nation ta ruwaito.

CBN ya kori karin ma'aikata 40

A wani rahoton kuma Wasu ma'aikatan babban bankin Najeriys (CBN) da suka kai mutum 40 sun rasa aikinsu bayan bankin ya ba su takardun kora.

Daga cikin waɗanda sabuwar korar ta ritsa da su akwai mataimakin darakta a CBN mai kula da sashen NCR.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel