Gwamnatin Neja Ta Umarci Jami'an Tsaro Su Harbe Duk Dan Daban da Aka Gani da Makami
- Gwamnatin jihar Neja ta amince da jami'an tsaro su harbe duk dan dabar da su ka gani yawo da muggan makamai a jihar
- An dauki matakin ne a tarom masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago
- Wannan matakin na zuwa ne bayan 'yan bindiga da yan daba sun matsa wajen kai hare-hare musamman kan masallata a 'yan kwanakin nan
Jihar Neja- Gwamnatin jihar Neja ta umarci jami'an tsaro su harbe duk wani ɗan daba da su ka yi ido huɗu da shi yana ɗauke da mugun makami.
An cimma wannan matsayar ce bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago kamar yadda daily trust ta ruwaito.
Da yake karin bayani, Shugaban karamar hukumar Chanchaga, Aminu Yakubu Ladan ya ce an ɗauki matakin ne domin bawa mazauna jihar damar gudanar da ayyukansu ba tare da fargaba ba.
Dalilin bayar da umarnin harbe ƴan daba
A ƴan kwanakin nan, ana samun karuwar ayyukan daba a Minna, babban birnin jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu rahotannin yadda ƴan dabar su ka kai hare-haren kan masallata yayin gudanar da sallar Tahajjud a watan Ramadan din nan.
Ladan ya ce gwamnati ba za ta zuba idanu yara marasa tarbiyya su hana al'umma zaman lafiya ba.
Masarautar Minna ta tabbatar da matakin
Musa Adamu Mai Kuɗi Achaza, jami'in hulda da jama'a na masarautar Minna ya tabbatar da amincewa da matakin bawa jami'an tsaro damar harbe duk wanda aka gani ɗauke da mugun makami a jihar Neja.
Ya ce tuni jami'an tsaro su ka fara bi gida-gida domin damƙe duk waɗanda ake zargi na da alaƙa da kai hari kan jama'ar garin da ba-su-ji-ba ba-su-gani ba.
Musa Adamu Mai Kuɗi ya ce za kuma a gurfanar da waɗanda aka kama gaban Shari'a domin hukunta su.
A cewarsa, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce an samu nasarar kama wasu daga cikin ɓata-garin.
Asali: Legit.ng