“Ka Mayar da Pam Matsayin Shugaban NCPC”: Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu

“Ka Mayar da Pam Matsayin Shugaban NCPC”: Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu

  • Ana ci gaba da samun ra'ayoyi mabambanta game da korar Yakubu Pam daga mukamin shugaban hukumar alhazai ta Kirista (NCPC)
  • Dattawan Arewa sun yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu da ta mayar da Pam mukaminsa
  • Kungiyar ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Abdul-Azeez Suleiman tare da neman ayi bincike a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta nuna damuwarta kan yadda aka tsige Rabaran Yakubu Pam daga mukaminsa Na shugaban hukumar alhazai ta Kirista (NCPC).

Dattawan Arewa sun yi magana kan tsige shugaban hukumar NCPC
Dattawan Arewa sun nemi Tinubu ya mayar da Rabaran Yakubu Pam mukaminsa. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

"An kori Pam ba bisa ka'ida ba" - NEF

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi, kungiyar NEF a cikin sanarwar da Abdul-Azeez Suleiman, kakakinta ya fitar, ta ce an yi korar ne ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun NEF ya ce dakatar da Pam da aka yi ta jefa al'umar Kirista da ma Musulmi na Arewa cikin zullumi.

Dattawan Arewa sun nuna damuwarsu kan yadda gwamanti ke tafiyar da lamuranta ba tare da dalilai ko yin wani gamsasshen bayani ba.

"A mayar da Pam mukaminsa" - NEF

Dattawan sun ce Rabaran Pam wanda ya kasance a kan mukamin na tsawon shekaru uku an tsige shi ne ba bisa ka'ida ba.

Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kyale Pam ya kammala wa'adinsa, kamar yadda jaridar The Nigerian Tribune ta ruwaito.

NEF ta kuma zargi gwamnatin Tinubu kan yadda ta maye gurbin Pam da wani daga Legas, a abin da ta kira kwace kujerar da ta dace da Arewa a kai ta kudu.

Sanarwar ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan

“Bamu hana ka murabus ba”: Kungiyar kwadago ta fusata, ta tura sako mai zafi ga Peter Obi

"Yanayin yadda aka watsar wa Rabaran Pam kayansa daga ofis abin cin zarafi ne da wulakanci. NEF na Allah wadai da wannan mataki."

NEF ta soki mayar da ofisoshi zuwa Legas

Idan ba a manta ba, a wani labarin Legit Hausa ta ruwaito cewa dattawan Arewa sun soki kudirin gwamnatin tarayya ta dauke manyan ofisoshi daga Abuja zuwa Legas.

NEF ta ce babu kyautawa ace gwamnati ta mayar da ofisoshin hukumar FAAN da wasu ofisoshi na bankin CBN zuwa Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.