Anguwanni 481 da Karin Kudin Wutar Lantarki Ya Shafa a Nijeriya, NERC Ta Lissafa Su

Anguwanni 481 da Karin Kudin Wutar Lantarki Ya Shafa a Nijeriya, NERC Ta Lissafa Su

  • Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta yi karin kudin wuta ga akalla anguwanni 481 da ke fadin kasar
  • Wadannan anguwanni su ake kira 'yan sahun farko a tsarin ba da wutar lantarki (Band A) wadanda ke samun wutar ta awa 20 a rana
  • Legit Hausa ta tattara bayani kan wadannan anguwanni da kuma yadda 'yan kasa za su iya gane su da sanin sunayensu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Nijeriya NERC, ta amince da karin kudin wuta ga anguwanni 481 da ke a sahun farko (Band A).

Anguwanni 481 a Najeriya ne ke samun wutar lantarki ta awa 24 a rana
Akalla mutane miliyan 1.9 ne ke karkashin anguwanni 481 da aka kara wa kudin wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamfanoni da jerin adadin anguwanni

Takardun da jaridar Vanguard ta samu daga hukumar sun nuna cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, AEDC, yana da anguwanni 107 a karkashinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ci kamfanin AEDC tarar N200m saboda zaluntar mutane wajen shan lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin rarraba wutar na Yola, YEDC, yana da anguwanni 15, kamfanin IKEDC na Ikeja na da 45, sai kamfanin Fatakwal mai anguwanni 43.

Kamfanin rarraba wutar ta naduna na da anguwanni 25; Kano na da 43; Ibadan na da 30; Jos na da 64; Benin kuma na da 44; kamfanin Eko na da 21 sai Enugu mai 44.

Tallafin wutar lantarki

Tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa na wutar lantarki ya ragu da Naira biliyan 137.07 duk wata. Hakan na zuwa yayin da aka kara kudin lantarki ga kwastomomi da kashi 230.

Jaridar This Day ta rahoto hukumar ta bayyana cewa, karin kudin wutar ga abokan hulda miliyan 1.9 a Band A ya zama dole bayan sauye-sauyen da aka samu wajen janye tallafin lantarki.

A cewar NERC, sabon farashin ya dogara ne akan hauhawar farashin kayayyaki da kashi 31.7% da kuma farashin canjin kudin waje na N1,463.3/$1.

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Anguwannin da ke karkashin Band A

Yadda za ka iya gane anguwannin shi ne ta hanyar ziyartar shafin yanar gizo na kamfanin rarraba wutar lantarki da kake karkashinsa.

Daga nan sai ka shiga 'customer service' wanda zai kai ka inda za ka shiga 'customer feeder information'.

Bayan ya bude maka sai ka shiga 'customer feeder verification', inda za ka saka lambar asusunka ko lambar mitar gidanka.

Shafukan kamfanonin lantarki

  • Ikeja: https://www.ikejaelectric.com/
  • Fakatwal: https://phed.com.ng/
  • Kaduna: https://kadunaelectric.com/
  • Kano: https://kedcoerp.com/
  • Ibadan: https://ibedc.com/
  • Jos: https://www.jedplc.com/
  • Benin: https://beninelectric.com/
  • Eko: https://ekedp.com/
  • Enugu: https://www.enugudisco.com/

Za a kuma kara kudin wutar lantarki

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin Nijeriya ta ce 'yan Najeriya su shirya biyan kudin lantarki da tsada.

A cewar ministan makamashi, Adebayo Adelabu wannan karin zai shafi kasar ne baki daya sakamakon yunkurin gwamnati na janye wa daga biyan tallafin wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.