Gwamna Zai Gwangwaje Iyayen 'Yar Bautar Kasa Ta NYSC da Katafaren Gida, Ya Ambato Dalilansa
- Wani faifan bidiyo na wata ƴar bautar ƙasa ta NYSC da ta karrama mahaifinta saboda sadaukarwarsa wajen ɗaukar nauyin karatunta ya sauya mata rayuwa
- Wannan faifan bidiyo ya ratsa zuciyar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, wanda ya yi mamakin lamarin
- Iyayen ƴar bautar ƙasar suna zaune ne a cikin wani tsohon gida, amma duk da haka ta iya nunawa duniya mahaifinta cike da alfahari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana shirin gina gida mai ɗaki uku ga iyayen wata ƴar bautar ƙasa ta NYSC.
Wannan matakin ya biyo bayan wani faifan bidiyo mai ratsa zuciya da ƴar bautar ƙasan ta NYSC ta nuna godiya ga mahaifinta bisa sadaukarwar da ya yi wajen samar mata da ilimi duk kuwa da yanayin rayuwa da suke ciki a wani tsohon gida.
Bidiyon ya zaburar da Gwamna Eno, wanda ya yi alƙawarin taimakon iyayenta saboda jajircewarsu wajen ganin ƴarsu ta samu ilmi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Uno zai gina gidan?
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da aka sanya a shafin X, na gwamnatin jihar Akwa Ibom da aka sanya a ranar Juma'a, 29 ga watan Maris 2024.
Ƴar bautar ƙasan dai da iyayenta sun fito ne daga jihar Kuros Ribas, mai makwabtaka da jihar Akwa Ibom.
A cikin faifan bidiyon, Mista Eno ya bayyana cewa wata tawaga daga gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ziyarci iyalan waɗanda ke a Kuros Ribas domin tantance su tare da fara gina musu gida.
Gwamnan ya bayyana cewa:
"Darasi cikin abin da yarinyar ta yi shi ne komawa cikin tsohon gidan kuma ta sa mahaifinta alfahari."
Uno na goyon bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ba zai yarda faɗan siyasa ya shiga tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.
Duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba, Gwamna Eno, mamban jam'iyyar PDP ya gargaɗi mambobin jam'iyyarsa su guji ɗabi'u mara kyau musamnam zagin jagororin siyasa.
Asali: Legit.ng