DHQ: Sojoji Sun Kashe Wasu Daga Cikin Ƴan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Kuriga

DHQ: Sojoji Sun Kashe Wasu Daga Cikin Ƴan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Kuriga

  • DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin haɗin guiwa sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigar da suka sace ɗaliban Kuriga 137
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa, Janar Buba, ya ce ba a kama ko ɗaya daga cikinsu ba amma an kubutar da ɗaliban
  • Ya jaddada cewa rundunar sojoji ba za ta yi ƙasa a guiwa ba a ƙokarin da take na tabbatar da zaman lafiya a sassan ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sojoji sun kashe wadanda suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a yayin ƙoƙarin ceto su.

An kubutar da ɗaliban su 137 a jihar Zamfara ranar 24 ga Maris 2024 bayan wani kazamin artabu da ‘yan ta’addan suka yi da sojoji tare da hadin guiwar ƴan sa'kai.

Kara karanta wannan

Okuama: Sarkin da ake nema ruwa a jallo ya koma hannun sojoji, ƴan sanda sun yi magana

Dakarun sojojin Najeriya.
DHQ ta ce an kashe wasu daga cikin waɗanda suka sace ɗaliban Kuriga Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Yadda sojoji suka ceto ɗaliban Kuriga

Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ), a wata sanarwa da ta fitar ta ce sojoji tare da hadin gwiwar hukumomin yankin ne suka ceto yaran, jaridar Leaderdhip ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaliban sun kuɓuta ne kwanaki 18 bayan sace su amma hukumomi ba su bayyana ko an biya kudin fansa ga ƴan bindigar ko ba a biya ba.

An kashe wasu daga ciki masu garkuwar

Amma mai magana da yawun DHQ, Janar Edward Buba, a wata hira ta musamman da jaridar Leadership a karshen mako, ya ce sojoji sun ceto ɗaliban ne a wani samamen haɗin guiwa.

Ya ƙara da cewa babu wanda aka kama daga cikin masu garkuwar amma dakarun sojin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ƴan bindigar.

Dangane da ko an kama wasu daga cikin ƴan ta'addan, Buba ya ce “an kashe wasu daga cikinsu a musayar wuta da sojoji, amma ba a kama ko ɗaya ba."

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini a Arewa ya tona manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan bindiga

Haka nan kuma a wata hira da manema labarai ranar Alhamis, kakakin DHQ ya ce rundunar sojoji ta duƙufa wajen ganin ta ci gaba da samun nasarori kan ƴan tada kayar baya.

A cewarsa, ceto almajiran Sakkwato da ɗaliban makarantar Kuriga a baya-bayan nan kaɗai ya nuna yadda dakarun sojoji suka shirya kawo ƙarshen ƴan ta'adda.

Wani abu ya fashe a Abuja

A wani rahoton kun ji cewa mutane sun shiga fargaba yayin da wani abu da ake zargin bam ne ya tashi a birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a.

Mazauna yankin sun ce abun ya fashe ne a ɗakin wasu mutum biyu maza, sun ce tukunyar gas ce amma babu wata alamar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262