Gaskiya Ta Fito, Shugaba Tinubu Ya Ba da Tallafin Makudan Kuɗi Domin Rage Kuɗin Hajji 2024

Gaskiya Ta Fito, Shugaba Tinubu Ya Ba da Tallafin Makudan Kuɗi Domin Rage Kuɗin Hajji 2024

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta tallafawa aikin hajjin bana da N90bn domin ragewa alhazai tsadar kuɗin kujera
  • Wata majiya daga hukumar NAHCON ta bayyana cewa wannan tallafin ne ya sa aka nemi alhazai su cika N1.9m amma da sai ƙarin ya wuce haka
  • A farkon makon nan ne hukumar NAHCON ta buƙaci alhazai su cika kuɗi bayan kuɗin da suna biya tun farko N4.9m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban kasa, Bola Tinubu, ta saki zunzurutun kudi har Naira biliyan 90 domin tallafawa aikin hajjin 2024.

Wata majiya mai tushe daga hukumar jin daɗin alhazai ta kasa (NAHCON) ce ta bayyana hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamnan PDP ya biya rabin kuɗin da aka ƙarawa mahajjatan jihar Arewa, ya faɗi dalili

Bola Ahmed Tinubu.
FG tarayya ta sanya tallafi a hajjin bana 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa idan ba don haka ba, da kowane mahajjaci sai ya kara akalla Naira miliyan 3.5 bayan N4.9m na farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ya tabbatar da cewa da gaske ne gwamnatin tarayya "ta ba da tallafin wasu kudi ga aikin hajjin bana."

Yadda aka samu ƙarin kuɗin hajji

Idan baku manta ba a watan Disamba, 2023, hukumar ta NAHCON a watan ta kayyade N4.9m a matsayin kuɗin kujerar hajji da kowane maniyyaci zai biya, lokacin ana canjin dala kan N897.

A wancan lokacin, hukumar ta sanar da kuɗin kujerar hajji N4,899,000 ga maniyyatan Kudu, N4,699,000 ga maniyyatan Arewa, yayin da na Yola da Maiduguri kuma za su biya N4,679,000.

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Usara ta fitar ranar Lahadin da ta gabata, ta kara N1,918,032.91, jimulla idan aka haɗa ya kai N6.8m.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya da suka ba alhazai tallafin kudin aikin Hajji

Meyasa aka ƙara kuɗin kujerar hajjin 2024?

Hukumar ta ce kowane alhaji yana da lokaci har zuwa jiya Alhamis (28 ga watan Maris, 2024) ya cika kuɗin zuwa aikin hajjin.

Hukumar NAHCON ta alakanta wannan ƙari da aka samu a kudin hajjin bana kan matsalar canjin Dala wanda Najeriya ta kwashe watanni tana fama da shi.

Majiyar NAHCON ta shaida wa Daily Trust cewa da a ce hukumar ta samu tallafin N230bn daga gwamnatin tarayya, ba za a buƙaci maniyyata su kara ko kwabo ba.

Yaushe gwamnatin Tinubu ta bada tallafin?

"Gwamnati ta sanar da bayar da tallafin N90bn a gaban ƴan jarida yayin rantsar da majalisar gudanarwa ta NAHCON a ofishin mataimakin shugaban ƙasa ranar 28 ga watan Fabrairu.
"To amma an gargaɗi ƴan jaridar kada su fitar da rahoton shiyasa babu jaridar da ta buga labarin, ko kun gani? Idan maniyyata suka ƙara N1.9m adadin ya cika cas."

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

- Cewar majiyar.

Tinubu ya yi buɗa baki da malamai

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya yi buɗa bakin azumi na 18 tare da manyan malamai da sarakuna a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.

Shugaban ƙasar ya roƙi malamai su guji zagin Najeriya a wurin wa'azi domin kasar ta su ce kuma addu'a ta fi buƙata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262