Buga Takardun Bogi: Kotun Abuja Ta Dauki Mataki Kan Sanatan PDP, Konbowei
- Babbar kotun tarayya da ke Apo, birnin Abuja ta fara daukar mataki kan Sanata Benson Konbowei da ake zargin ya buga takardun bogi
- A ranar Talata ne aka gurfanar da Konbowei kan tuhume-tuhume uku, da suka hada da buga takardar NYSC ta bogi da amfani da ita
- A zaman kotun na yau Alhamis, Mai shari'a Christopher Oba, ya bayar da sanatan beli a kan N50m, tare da turasa zuwa gidan yarin Kuje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotun birnin tarayya da ke Apo ta bayar da belin sanatan PDP mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya, Benson Konbowei, a kan N50m.
An gurfanar da sanatan a ranar Talata a kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da buga takardar shaidar NYSC ta bogi da dai sauransu.
An nemi belin Sanatan Konbowei
Talabijin na AIT ya ruwaito cewa kotun ta amince Konbowei ya koma gida har sai an yanke hukunci kan bukatar neman belinsa da aka sanya ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai lauyan mai gabatar da kara, Rubben Egwaba, ya ki amincewa da neman belin wanda ake tuhuma.
Ya bayyana cewa wanda ake kara zai iya yin katsalandan a tuhumar da ake yi masa idan har aka bayar da shi beli.
A bangaren wanda ake kara, talabijin na Channels ya ruwaito Gordy Uche (SAN), ya tabbatarwa kotun cewa Konbowei ba zai tsallake ka'idar belin ba idan har aka ba shi.
Matakin da kotu ta dauka
Da yake yanke hukunci kan neman belin, alkalin kotun, Christopher Oba, ya bayar da belin wanda ake karar a kan N50m.
Bugu da kari, ya ce dole ne wanda ake kara ya bayar da masu tsaya masa guda biyu da ke da kadarori a cikin babban birnin tarayya.
Sai dai ya bayar da umarnin a tsare Sanatan a gidan gyaran hali na Kuje har sai ya kammala cika sharuddan belin.
Kotu ta wanke tsohon minista
A wani labarin kuma, Legit ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta wanke tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke daga zargin karbar rashawa.
Tun a 2020 ne hukumar EFCC ta ke tuhumar Adoke da karbar Naira miliyan 300 daga hannun wani Aliyu Abubakar a harkar man Malabu.
Asali: Legit.ng