Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Ya Daina Zuwa Makaranta Saboda Ya Burge Ƴan Matan Garinsu
- Sanata Tahir Monguno ya ba da labarin yadda ya daina zuwa makaranta domin ya riƙa burge ƴan mata a garinsu da ke jihar Borno
- Monguno, mai wakiltar Borno ta Arewa ya bayyana haka yayin da yake jawabi a zauren majalisar dattawa kan kudirin yaran da ba su zuwa makaranta
- A cewarsa, domin ya zama ɗaya daga cikin waɗanda ƴan mata suka fi so a al'adar garinsu ne ya ɗauki wannan mataki lokacin yana firamare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Tahir Monguno, ya ce ya daina zuwa makaranta a lokacin da yake karatun firamare saboda yana son ya zama abin sha'awa ga 'yan mata a yankinsa.
Monguno, 'dan jam'iyyar APC ya ce al'adar ƙauyensu ce ta sa ya daina zuwa makaranta domin ya ja hankalin ƴan mata.
A cewarsa, al'adar ta bai wa mata damar zaɓo mazan da suke direbobi domin su yi nishaɗi da rawa tare da su a wannan lokaci, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce domin ya zama daya daga cikin wadanda ‘yan matan suka fi so su yi rawa da nishadi da su shiyasa ya daina zuwa makarantar firamare ya kama tuƙi a ƙauyensu.
Sanata Monguno ya ba da wannan labarin ne a zauren majalisar dattawa lokacin da yake ba da gudummuwa a kudirin da Sanata Adebule Oluranti (APC, Legas ta Yamma) ya gabatar.
Kudirin dai ya bukaci majalisar dattawan ta lalubo hanyoyin daƙile ƙaruwar yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
'Dalilin daina zuwa makaranta'
"Na yanke cewa wani abu a wannan kudirin ne saboda abin da ya faru a rayuwata lokacin da nake tasowa. Lokacin ina aji 7 a firamare, bisa ra'ayin kaina na daina zuwa makaranta.
"Dalilin da ya sa na daina zuwa makaranta shi ne saboda a garin mu a wancan lokacin kowa so yake ya zama direba, da zaran ka zama direba shikenan ka zama ɗaya daga cikin manyan gari.
"Muna da wata al'ada a lokacin, a al'adar maza da mata za su zo suyi layi, ƴan mata za su zaɓi mazan da za su yi rawa da su. To matan direbobi kaɗai suke ɗauka, ba ruwansu da mu.
"Ganin hake na ce tun da haka abin yake bari na koma na zama direba saboda idan an zo wurin wannan wasan mata su zaɓe ni mu yi rawa. Saboda haka na daina zuwa makaranta."
- Tahir Monguno.
Meyasa sanatan ya ba da labarin?
Monguno, wanda a yanzu ya zama lauya, ya ce ya yi sa'ar komawa makaranta domin kawunaa ne ya dage cewa dole ne ya samu ilimin zamani.
Sanatan ya ba da labarin rayuwarsa ta farko ne domin nuna rashin dacewar yaran da ke barin karatun boko don biyan wasu bukatusu na daban, rahoton jaridar Tribune.
Tinubu ya sha ruwa da sanatoci
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido ta yi shiru ba kan kisan dakarun sojoji a jihar Delta.
Yayin da ya karɓi bakuncin sanatoci a wurin buɗa baki, Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a Okuama za su ɗanɗana kuɗarsu.
Asali: Legit.ng