Gwamnan APC Ya Raba Tallafin Maƙudan Kuɗi Ga Mutanen da Matsaloli 2 Suka Shafa a Jihar Arewa

Gwamnan APC Ya Raba Tallafin Maƙudan Kuɗi Ga Mutanen da Matsaloli 2 Suka Shafa a Jihar Arewa

  • Malam Dikko Radda ya rabawa mata da ƴan matan da hare-haren bindiga ya shafa tallafin N150,000 domin su fara sana'a
  • Gwamnan Katsina ya kuma raba tallafin N100,000 ga iyaye mata da ƴan matan da cutar korona ta durkusar da kasuwancinsu a kananan hukumomi 34 na Katsina
  • Radda ya shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace domin su amfanar da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radɗa, ya raba tallafin N470m ga mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa da waɗanda cutar korona ta gurgunta.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Mohammed Kaula ya fitar a Katsina.

Kara karanta wannan

A karo na biyu, gwamnan Arewa ya fara raba tallafin kuɗi da abinci na N11.4bn a jiharsa

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Gwamna Radda Ya Rabawa Mutanen da Harin Yan Bindiga Ya Shafa Tallafi a Katsina Hoto: Isah Miqdad
Asali: Facebook

Kaula ya ce shirin ya samu haɗin guiwar hukumar ba da agaji ta duniya da kamfanin R.H. Equipt da nufin ragewa waɗannan mutanen raɗaɗin halin da suka tsinci kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tallafin kuɗin da Raɗɗa ya rabawa matan

A wurin kaddamar da shirin a Katsina, Gwamna Raɗda ya bayyana cewa mata 550 da hare-haren ƴan bindiga ya shafa sun samu tallafin N150,000 kowanensu, jimillar kudin shi ne N82.5m.

A cewarsa, an zaɓo iyaye mata da ƴan mata 114 daga kananan hukumomi 34 na Katsina, waɗanda annobar cutar korona ta kassara kasuwancinsu, inda aka tallafawa kowace daga ciki da N100,000.

Babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin sadarwa na zamani, Isah Miqdad, ya tabbatar da haka a shafinsa na Manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Gwamna Raɗda ya cika alkawarin kamfe

Gwamna Raɗɗa ya ce wannan shirin tallafin na ɗaƴa daga cikin alƙawurran kamfen da ya yi a wurin muhawarar da BBC ta shirya a watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fitar da maƙudan kuɗi domin rabawa talakawa abinci kyauta a Ramadan

Dikko ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da karfafa wa wadanda rikicin ‘yan bindiga da kuma annobar COVID-19 ya shafa, musamman mata da ‘yan mata.

Gwamna Radda ya yabawa ma’aikatar noma da kiwo ta jihar Katsina da kuma majalisar dokokin jihar bisa rawar da suka taka wajen zabo da horar da wadanda suka ci gajiyar tallafin.

Dukkan matan da suka ci gajiyar shirin sun samu horo kan sana'o'i daban-daban, bisa haka gwamnan ya ba su shawarin su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ya dace.

Ramadan: Za a ciyar da miliyoyin mutane

A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara shirin ciyar da mabuƙata abinci kowace rana a watan Ramadan.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Baba Ɗantiye, ya ce gwamnati ta ware wa shirin ciyarwa na watan Ramadan N6bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262