Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Ware Makudan Kuɗi Domin Ciyar da Mabuƙata a Watan Ramadan
- Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara shirin ciyar da mabuƙata abinci kowace rana a watan Ramadan
- Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Baba Ɗantiye, ya ce gwamnati ta ware wa shirin ciyarwa na watan Ramadan N6bn
- Ya ce kuɗin sun kunshi na kayan abinci, itacen girki, tsaro da na masu girkin da za su yi aiki na tsawon watan azumi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ciyar da mutane miliyan hudu a watan Ramadan na 1235H/2024 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Baba Dantiye ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Leadership a Kano, jiya Litinin.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 6 domin ciyar da marasa galihu a jihar da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka tsara ciyarwa a Kano
Kwamishinan ya ce birnin Kano mai tulin jama'a wanda ya kunshi kananan hukumomi takwas yana da cibiyoyi na musamman guda 90 na ciyarwa a watan azumi.
A cewarsa, cibiyoyin cikin birni da gwamnati ta ware domin ciyar da talakawa da gajiyayyu sun haɗa da masallatai, kurkuku, tsangaya, asibitoci da makarantun islamiyya.
Ya ce ana sa ran za a rabawa mutane 18,000 abinci kowace rana har ƙarshen watan azumin Ramadan.
Ya ce kudin da aka ware ya haɗa da kuɗin kayan abinci, hayar kayan girki, alawus-alawus na dafa abinci da tsaro, itacen wuta da dai sauran su na tsawon watan.
Adadin da aka ware wa kowace cibiya
"A kowace cibiya muna da mata uku masu dafa abinci da kuma maza uku wadanda ke samar da tsaro don ka da mutane su yi wawa su haifar da turereniya.
"Haka nan kuma a kowace cibiya an ware buhunan shinkafa biyu don ciyar da mutane akalla 200, wato mutum 100 a kowace buhu. Akwai nau’o’in abinci irin su wainar wake, koko da sauran abinci iri-iri da ake dafawa a kullum.
"Sannan ana fito da abincin a raba tsakanin karfe 6:30 na yamma zuwa karfe 7:00 na yamma kuma an fi maida hankali kan mabuƙata."
- Baba Ɗantiye.
Tun da farko dai gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai kula da shirin ciyarwa a Ramadan wanda mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam ya kaddamar, The Cable ta rahoto.
Abba Kabir ya ƙara rusau a Kano
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta take umarnin kotu, ta ci gaba da rusau a yankin ƙaramar hukumar hukumar Kunbotso
Hukumar tsare-tsare da raya birane ta Kano KNUPDA ta rushe wasu gidaje a garin Gurin Gawa ranar Lahadin da ta gabata.
Asali: Legit.ng