Gwamnan APC Ya Ayyana Hutun Kwanaki 5, Ya Fadi Dalili

Gwamnan APC Ya Ayyana Hutun Kwanaki 5, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayar da hutun kwanaki biyar domin rabon kayan tallafi a watan Ramadan
  • Mai girma Bago ya ce hutun zai kasance ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Maris har zuwa ranar Juma'a, 22 ga watan Maris
  • Gwamnan na Neja ya bayyana cewa kayan tallafin za a raba su ne domin rage raɗaɗin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Minna, jihar Neja - Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ayyana ranar Litinin, 18 ga Maris zuwa Juma’a 22 ga Maris a matsayin ranakun hutu.

Umar Bago ya ce hutun na rarraba kayan tallafi ne da ciyarwa a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya canza tunani, ya janye sunan matar da ya naɗa a babban banki CBN, An gano dalili

Gwamna Bago ya bada hutu
Gwamna Bago ya ayyana hutun kwanaki biyar a Neja Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishiniyar yaɗa labarai, Honorabul Binta Mamman, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Bago ya bada hutu a Neja?

Kwamishiniyar ta ce an bada hutun ne domin ba ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa damar sa idon kan yadda za a yi rabon a ƙananan hukumominsu.

Gwamnan ya bayyana cewa za a raba kayayyakin tallafin a faɗin jihar ta yankin Arewa ta Tsakiya domin rage raɗaɗin taɓarɓarewar tattalin arziƙin da ake fama da ita a ƙasar nan.

Mamman ta bukaci jama’a da su baiwa jami’ai haɗin kai tare da kasancewa cikin tsari a duk wuraren yin rabon da ciyarwar domin gudanar da aikin cikin nasara.

Ta shawarci ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa da su ɗauki wannan aiki a matsayin lokacin yi wa jama'a hidima.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Tinubu na bada tallafin N500,000 ga matasa? Gaskiya ta bayyana

Bago da hutun rabon abinci a Neja

Wannan dai ba shi ne karon farko da Gwamna Bago ya ayyana hutu ba domin rabon kayan abinci a jihar.

A baya gwamnati ta ayyana hutun kwanaki uku a watan Satumban 2023, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ma'aikata sun samu ƙarin albashi a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya shirya faranta ran ma'aikata a jihar.

Gwamnan ya amince da bayar da tallafin albashin N20,000 ga dukkanin ma'aikatan gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng