Abin sha'awa: Bola Tinubu Ya Yi Buɗe Baki 'Iftar' Na Azumin Ramadan Tare da Wasu Gwamnoni a Villa
- Bola Ahmed Tinubu ya yi buɗa bakin azumi na hudu a watan Ramadan na 1445H/2024 tare da wasu gwamnoni a Villa
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, shugaban ma'aikatan fadar gwamnati da ministan Abuja sun halarci Iftaar ranar Alhamis
- Farfesa Babagana Zulum na Borno da Malam Uba Sani na Kaduna suna daga cikin gwamnonin da suka sha ruwa a fadar shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi buɗe baki watau Iftar na azumin watan Ramadan tare da wasu gwamnoni yau Alhamis, 14 ga watan Maris.
Kamar yadda The Nation ta tattaro, mafi akasarin gwamnonin sun halarci wurin buɗe baki da shugaban ƙasa a ɗakin taro na Aso Villa.
Sauran manyan ƙusoshin gwamnatin Najeriya da suka halarci Iftar sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya halarci buɗe bakin a ranar Musulmi suka kai azumi na huɗu a 1445AH.
Ramadan: Gwamnonin da suka je Iftar a Villa
Gwamnonin da suka halarci wurin buɗe baki da Tinubu sun haɗa da AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Sheriff Oborevwori (Delta) da Hyacinth Alia (Benuwai).
Sauran sun kunshi Caleb Mutfwang (Filato), Ahmed Ododo (Kogi), Nasir Idris (Kebbi), Bala Mohammed (Bauchi), Farfesa Babagana Zulum (Borno) da Douye Diri (Bayelsa).
Sai kuma Dapo Abiodun (Ogun), Abdullahi Sule (Nasarawa), Francis Nwifuru (Ebonyi), MuhammadInuwa Yahaya (Gombe), da Alex Otti (Abia), rahoton Arise TV.
Godwin Obaseki (Edo), Malam Uba Sani (Kaduna) da kuma Agbu Kefas (Taraba) duk sun halarci baƙi bakin azumi na huɗu tare da mai girma shugaban ƙasa.
Shugabar majalisar dattawa zai yi murabus?
A wani rahoton na daban kun ji cewa Majalisar dattawa ta mayar da martani ga jam'iyyar PDP kan kiran da ta yi na cewa Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus
Shugaban kwamitin yaɗa labarai, Yemi Adaramodu, ya ce Akpabio ba zai sauka daga shugabancin majalisar dattawa ta 10 kamar yadda PDP ta buƙata ba
Asali: Legit.ng