Hukumar Shige da Fice Ta Magantu Kan Umarnin Tinubu Na Bude Iyakar Najeriya da Nijar

Hukumar Shige da Fice Ta Magantu Kan Umarnin Tinubu Na Bude Iyakar Najeriya da Nijar

  • Hukumar shige da fice ta kasa ta ce za ta gaggauta bin umarnin Shugaba Bola Tinubu na bude iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar
  • Kwanturola Janar ta hukumar shige da fice ta kasa, Kemi Nanna Nandap ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis
  • Nandap ta kuma bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin bin ka’idoji yayin shige da fice a iyakokin kasashen biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kwanturola Janar ta hukumar shige da fice ta kasa, Kemi Nanna Nandap, ta umurci dukkan shugabannin hukumar da su yi gaggawar bin umarnin Shugaba Bola Tinubu na bude iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin 2024: PDP ta bukaci Akpabio ya yi murabus, an samu karin bayani

Ga masu ruwa da tsaki a ayyukan hukumar, Nandap ta kuma ba su tabbacin bin matakan da suka dace yayin shige da fice a iyakokin kasashen biyu.

Hukumar shige da fice yi martani kan umarnin Tinubu na bude iyakokin Nijar
Hukumar shige da fice ta fitar da sanarwa kan bude iyakar Najeriya da Nijar. Hoto: @nigimmigration
Asali: Twitter

Umarnin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin Nandap, Kenneth Kure, ya fitar a ranar Alhamis, 14 ga Maris, 2024 a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nijar: "A gaggauta bin umarnin Tinubu" - Nandap

Sanarwar da Kure ya fitar na dauke dataken:

"CGI Nandap ta ba da umarnin a gaggauta na a aiwatar da umarnin shugaban kasa na bude iyakokin Niger."

Kure ya ce akwai bukatar daukar mataki cikin gaggawa domin aiwatar da wannan umarni da Tinubu ya bayar.

Sanarwar ta ce:

"Hukumar shige da fice ta Najeriya tana ba al'umma tabbacin cewa tana aiki tukuru domin samar da tsari mai kyau na tsallaka kan iyakokin Najeriya da tabbatar da tsaro a iyakokin kasar."

Kara karanta wannan

Yayin da ake cikin wani hali, Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya, bayani sun fito

Gwamnati ta dage takunkumin Nijar

A ranar Laraba ne mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa gwamnati ta dage takunkumin da ta kakabawa jamhuriyar Nijar.

Ngelale a cikin sanarwar ya ce:

“Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin kasa da sama na Najeriya da jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumi da aka sanyawa kasar, nan take.
“Wannan umarnin ya yi daidai da shawarar da hukumar ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja."

ECOWAS ta dage takunkumin kasashe 3

Tun da fari, Legit ta ruwaito cewa kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta sanar da dage takunkumin da ta kakabawa Nijar, Mali da Burkina Faso.

ECOWAS ta kakaba wa ƙasashen akalla takunkumi 8 biyo bayan juyin mulkin soja da aka yi a kasashen.

Sai dai daga baya ƙasashen sun yi barazanar ficewa daga kungiyar ta ECOWAS, lamarin da masu fashin baki ke ganin zai haifar da babbar illa a kasashen Afrika ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.