Rashin Tsaro: 'Yan Sanda Sun Samu Sabon Umurni a Jihar Kano

Rashin Tsaro: 'Yan Sanda Sun Samu Sabon Umurni a Jihar Kano

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta zage damtse domin samar da cikakken tsaro ga makarantun da ke faɗin jihar
  • Kwamishinan ƴan sanda a jihar ya umurci jami'an rundunar da su ƙara yawan sintirin da suke gudanarwa
  • Umurnin na zuwa ne a yayin da ake samun matsalar sace ɗalibai da malamai a wasu jihohin da ke Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Hussaini Gumel, ya umurci jami'an rundunar ƴan sandan jihar da su ƙara zage ɗamtse wajen samar da tsaro.

Kwamishinan ya umurci kwamandojin shiyya-shiyya da DPO na ƙananan hukumomi, da su ƙara yawan sintirin da suke yi a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu a jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama hatsabiban masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a Arewa

'Yan sanda sun samu sabon umurni a Kano
CP Gumel ya umurci a gudanar da sintiri a makarantun Kano Hoto: @KanoPoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar The Guardian ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, ya fitar ranar Laraba, 12 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa rundunar 'yan sanda ta ɗauki matakin?

Ya ce matakin ya yi daidai da umarnin babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, kan tabbatar da tsaro a makarantu.

Haruna ya ce wannan umarni na da nufin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi, musamman tsaron makarantu da ɗalibai.

A kalamansa:

"Matakin na da nufin tabbatar da tsaro ga ɗalibai, malamai da ma'aikata da kuma bunƙasa fannin ilimi gaba ɗaya a jihar.
"Manufar ƙara yawan jami'an ƴan sanda a waɗannan wuraren shi ne don ƙara daƙile aikata laifuffuka da samar da ingantaccen yanayin bada ilmi.

Ya buƙaci jama’a musamman shugabannin makarantu, malamai, iyaye da ɗalibai da su ba ƴan sanda da sauran jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba don ɗaukar matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Ramadan: Rundunar ƴan sanda ta aike da saƙo mai muhimmanci ga musulmai a Najeriya

An hana ƴan sanda aiki da POS a ofis

A wani labarin kuma, kun ji cewa sufeto janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya hana amfani da na'urar POS a cikin harabar ofisoshin ƴan sanda dake faɗin ƙasar nan.

Umurnin Egbetokun na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi kan cewa wasu gurɓatattun jami'an ƴan sanda na haɗa baki da masu POS suna zaluntar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng