Sokoto: Ƴan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Ɗaliban Makarantar Alƙur'ani Sun Turo Saƙo Mara Daɗi

Sokoto: Ƴan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Ɗaliban Makarantar Alƙur'ani Sun Turo Saƙo Mara Daɗi

  • Miyagun ƴan bindigan da suka yi garkuwa da almajirai a jihar Sakkato sun kira wayar malamin tsangaya ranar Talata
  • Malamin makarantar, Liman Abubakar, ya ce maharan sun nemi a tattara masu Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan ƴan bindiga sun sace almajirai 16 a garin Gidan Bakuso, ƙaramar hukumar Gada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - ‘Yan bindigan da suka sace almajirai 16 a makarantar koyar da karatun Alkur’ani a jihar Sokoto sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 20.

Shugaban makarantar wadda aka fi sani da Tsangaya, Liman Abubakar, ne ya bayyana hakan ga wakilin jaridar Daily Trust a ranar Talata, 12 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki asibitin jami'ar tarayya, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

Gwamna Ahmad Aliyu na Sokoto.
Halin da almajiran da ƴan bindiga suka sace ke ciki Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Twitter

Malamin ya ce masu garkuwan sun kira shi sau biyu da safiyar nan kuma sun tambaye shi kan ko bai damu da almajiransa bane, sannan suka faɗi buƙatarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ƴan bindigan suka buƙata?

"Sun kira ni ta wayar tarho sau biyu yau da safe (ranar Talata da safiya). A kiran farko sun tambaye ni ko ban damu da halin da almajirai na ke ciki ba ne shiyasa ban neme su ba.
"Na faɗa musu bani da lambar wayarsu, daga nan sai suka faɗa mani na saurari kira na biyu da ƙarfe 11:00 na safe.
Bayan karfe 11:00 ta gota sai suka kira ni suka umarci na je wurin magajin gari na faɗa masa a tara masu N20m."
"Na so in roƙi su rage kuɗin amma suka ce ba za su rage komai daga kudin ba. Na tashi na je wurin magajin gari muka tattauna kan batun amma har yanzu ba mu kai ga cimma matsaya ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nemi Naira tiriliyan 40 da abu 2 a matsayin kuɗin fansar mutane 16 a jihar Arewa

- Liman Abubakar.

Yadda aka yu garkuwa da almajirai a Sokoto

Ƴan bindiga sun sace almajiran ne a kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada a ranar Asabar din da ta gabata, The Cable ta rahoto.

Rahoto ya nuna maharan sun tafi da almajiran ne a lokacin da suke ƙoƙarin guduwa zuwa dakunansu domin gujewa harin da aka kai garin.

Ƴan bindiga sun kai hari UNTH

A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun kai farmaki asibitin koyarwa na jami'ar tarayya ta UNTH a jihar Enugu da ke Kudu maso gabashin Najeriya.

Wasu majiyoyi daga asibitin sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da mataimakiyar darakta da kuma jami'in tsaro ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262