“Akwai Fa’idodi a Zaman Najeriya”: Budurwa Da Ke Zaune a Turai Ta Fadi Wahalhalun da Suke Sha
- Wata matashiyar budurwa a turai ta ce akwai wasu illoli da ke tattare da tafiya kasashen waje da zama a can
- A cewarta, mutane da ke zaune a Najeriya suna more wasu abubuwa da takwarorinsu na turai basa morewa
- Ta ce yayin da mutum ke iya yin fitsari a duk inda yake so a Najeriya, irin hakan ba mai yiwuwa bane a kasar da take da zama
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wata matashiya ta lissafa wasu fa'idodi da alfanun da ke tattare da zaman Najeriya maimakon turai.
Matashiyar ta wallafa bidiyon a shafinta na TikTok, @rca228, sannan ta bayyana cewa akwai alfanu sosai a zaman Najeriya.
A cewarta, yayin da mutanen da ke zaune a Najeriya za su iya more wasu abubuwa, kamar su fitsari a waje, wadanda ke turai ba za su iya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta jaddada cewar wadanda ke Najeriya za su iya gaggauta shiga daji don yin bahaya, amma hakan ba mai yiwuwa bane a turai.
Saboda haka, ta fada ma mutanen da ke zaune a Najeriya da su ji dadin damammakin da suke da su wadanda 'yan turai basu da iko a kansu.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@oluebube ya ce:
"Kada ki damu kwannan nan za a koro ki da izinin Allah, kawai ki ce amin."
@chijiokeadinnu ya ce:
"Ki dawo mana idan kin san kin haifu da kyau hajiya."
@BigBee ya ce:
"Toh me yasa kike a UK kenan?"
@YO FaVe BF ya ce:
"Naija ta fi dadi amma babu kudi."
@Tonia ta ce:
"Kana iya hawa babur a gaban gidanka amma a UK sai ka taka zuwa tashar mota."
@Spareparts_JB ya ce:
"Laifi ne a Najeriya ma, kawai dai ba a aiwatar da dokar yadda ya kamata ne."
'Dan Najeriya ya samu kyautar miliyan 159
A wani labarin, wani 'dan Najeriya ya taki babban sa'a saboda Allah ya tarbawa garinsa nono a lokacin da bai da ko sisi a turai.
Mutumin mai suna Kayode yana a dakin ajiye litattafai yana karatu lokacin da wani mai watsa shirye-shirye a intanet, Zachery Dereniowski ya neme shi.
Asali: Legit.ng