'Yar Jarida Ta Bayyana a Shirin Kai Tsaye da Goyo a Bayanta, Ta Karanto Labarai Cike da Kwarin Gwiwa
- Wata mai gabatar da shirye-shirye a gidan Talbijin, Kapinga Kisamba Clarisse ta nuna jajaircewa mai ban mamaki ta hanyar kawo jaririnta wajen aiki
- Wani bidiyo mai tsuma zuciya ya nuna 'yar jaridar tana karanto labarai tare da 'danta goye a bayanta
- Jama'a sun jinjinawa yadda Clarisse ke aiki da taka rawarta na uwa, suna masu jaddada muhimmancin tallafawa iyaye mata masu aiki
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Masu iya magana kan ce soyayyar uwa ga 'ya'yanta bai da iyaka. Kuma uwa mutum ce mai juriya, jajircewa da tsayin daka akan 'ya'yanta ba tare da gajiyawa ba.
A wani yanayi mai tsuma zuciya da ke tabbatar da gaskiyar hakan, wata mata ta dauka hankalin duniya ta hanyar hada matsayinta na uwa da aiki.
Hada aiki da raino
Kapinga Kisamba Clarisse, wata mai gabatar da shirye-shirye a gidan talbijin a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC), ta nuna jajircewa da azama da jarumtar ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Labarinta ya bayyana a tauraron 'dan adam, inda ta bayyana goye da yaronta a baya yayin da take karanto labarai.
Hoton Clarisse tana karanto labarai cike da kwarin gwiwa a ranar Juma'a, 8 ga watan Maris, goye da 'danta a baya wani al'amari ne mai girma.
Nan take bidiyon labaran da Clarisse ta gabatar ya karade soshiyal midiya, inda ya haifar da martani daga jama'a a fadin duniya.
Martanin jama'a kan bidiyon matar
@BahatiDjoki:
"Ya yi kyau, kawai suna nuna yadda suke da juriya."
@josephrukara:
"Uwa na da mutunci sosai. Rayuwa ba tare da uwa ba yana da matukar ziow. Allah ya albarkaci wannan mai gabatarwar."
@KINDELEMT11:
"Juriya ga matan mu."
@The_Guerilla_DJ:
"Tana da ban sha'awa!"
@PEREZMWETEISE1:
"Ba zan iya gajiya da kallon wannan bidiyo ba. Allah ya albarkaci matar da dukka iyaye mata a fadin duniya."
Budurwa ta kashe miliyan 1.9 kan turarruka
A wani labari na daban, wata matashiya ta ba da labarin kasaitaccen siyayya da suka je ita da kawarta suka yi.
Yan matan biyu sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 1.9, tama mai cewa suna matukar son kamshi.
Asali: Legit.ng