Ramadan 2024: Jerin Kasashen da Musulmai Za Su Yi Azumi Mafi Tsawo da Gajarta
- Watan azumin Ramadan na bana zai fara ko dai a ranar Litinin, 11 ga watan Maris ko Talata, 12 ga watan Maris, gwargwadon ganin jinjirin wata
- Azumin watan Ramadan yakan kasance daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana, inda ake samun bambancin tsawon sa'o'in yinsa daga 12 zuwa 17 a faɗin duniya
- A Najeriya, ana sa ran musulman da ke babban birnin tarayya Abuja za su yi azumi na kimanin sa'o'i 13
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Watan Ramadan, wata mai alfarma wanda ake gudanar da azumi, zai fara ne a ranar Litinin, 11 ga watan Maris ko Talata 12 ga watan Maris, gwargwadon ganin jinjirin wata.
Majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya NSCIA ta buƙaci al’ummar Musulmi da su duba injirin watan Ramadan 1445 a ranar Lahadi 10 ga watan Maris, daidai da 29 ga watan Sha’aban 1445 bayan hijira.
Ana yin azumin watan Ramadan ne daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana kuma yana ɗaukar sa'o'i 12 zuwa 17, ya danganta da wane ɓangare mutum yake zaune a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da Musulmai a ƙasashen da ke Arewacin duniya za su yi azumi mai tsawo, ƙasashen da ke Kudancin duniya za su yi sa'o'i ƴan kaɗan wajen yin azumi, cewar rahoton jaridar Aljazeera.
Ramadan 2024: Ƙasashen da za su yi azumi mai tsawo
- Nuuk, Greenland - Sa'o'i 17, mintuna 52
- Reykjavik, Iceland - Sa'o'i 17, mintuna 25
- Helsinki, Finland - Sa'o'i 17, mintuna 9
- Stockholm, Sweden - Sa'o'i 16, mintuna 47
- Glasgow, Scotland - Sa'o'i 16, mintuna 7
Ramadan 2024: Ƙasashen da za su yi azumi mara tsawo
- Christchurch, New Zealand - Sa'o'i 12, mintuna 42
- Puerto Montt, Chile - Sa'o'i 12, mintuna 43
- Canberra, Ostiraliya - Sa'o'i 12, mintuna 46
- Montevideo, Uruguay - Sa'o'i 12, mintuna 47
- Cape Town, Afirka ta Kudu - Sa'o'i 12, mintuna 48
Ramadan 2024: Lokacin azumi a Najeriya
Ana sa ran Musulmi a Abuja, babban birnin Najeriya za su yi azumi na kimanin sa'o'i 13.
A halin da ake ciki, idan aka ga jinjirin wata a ranar Lahadi da yamma, Sarkin Musulmi, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar zai ayyana ranar Litinin 11 ga watan Maris a matsayin ranar farko ta watan Ramadan 1445AH a Najeriya.
Amma idan ba a ga jinjirin watan a ranar Lahadi ba, to ranar Talata 12 ga Maris, zs ta zama farkon watan Ramadan, 1445AH.
Za a yi azumi sau biyu a 2030
A wani labarin kuma, kun ji cewaa, musulmai za su yi azumin Ramadana sau biyu a shekara ta 2030, kamar yadda wasu masana ilmin taurari suka yi hasashe.
Masana sun ce watan azumi zai shigo sau biyu a wannan shekara ta 2030, na farko a watan Janairu, sannan kuma a ƙarshen watan Disamba, lamarin da ya taba faruwa a shekarar 1997.
Asali: Legit.ng