Wasu Daga Cikin Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Kubuta Daga Hannun 'Yan Bindiga
- An shiga murna bayan da wasu daga cikin ƴan makarantar da aka sace a Kuriga ta jihar Kaduna suka kuɓuta daga hannun ƴan bindiga
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayar da tabbacin cewa ɗalibai 28 daga cikin waɗanda aka sace sun kuɓuta
- Kuɓutar ɗaliban dai babbar nasara ce ga ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ganin cewa an ceto dukkanin ƴan makarantan waɗanda yawansu ya wuce 200
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ɗalibai 28 daga cikin sama da 200 da ƴan bindiga suka sace a Kaduna sun tsere daga hannun miyagun.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, shi ne ya tabbatar da kuɓutar ɗaliban yayin tattaunawa da jaridar BBC Hausa.
Ba a dai bayyana yadda yaran suka samu suke tsere ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko gwamnan ya je filin jirgin sama na Kaduna a jiya domin tarbar mataimakin shugaban ƙasa Shettima tare da raka shi taro da iyayen yaran da aka sace.
Shettima ya bada tabbacin za a ceto yaran
A jawabin da ya yi gabanin ci gaba da taron a bayan fage, Shettima ya tabbatar wa iyayen yaran cewa gwamnati ta ƙudiri aniyar ganin an ceto dukkan yaran da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Ya shaida musu cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar cewa an ceto yaran, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa lura da rahotannin da suke bayarwa game da lamarin.
A kalamansa:
"Na zo nan ne bisa umarnin mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kaduna kan abin baƙin ciki na sace yaran makarantarmu.
"Shugaban kasa ya ji takaicin abin da ya faru kuma ya umurci jami’an tsaro cewa su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an ceto yaran an miƙa su hannun iyayensu.
"Shugaban ƙasan ya yi magana da gwamnan Jihar Kaduna sau hudu. Ya yi magana da ni sau uku game da ceto yaran."
Uba Sani ya hango kuskure a hanyar magance rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da ƙasar nan ke fuskanta a yanzu.
Uba Sani ya ce shugabannin siyasa a Najeriya sun biyo hanyar da ba daidai ba wajen kawo ƙarshen waɗannan manyan ƙalubalen guda biyu.
Asali: Legit.ng