Bayan Ganduje Ya Zama Shugaban APC, Ɗansa Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Bayan Ganduje Ya Zama Shugaban APC, Ɗansa Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Yayin da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ke sheke ayarsa a gwamnati, Bola Tinubu ya sake nada ɗansa mukami
  • Shugaba Tinubu ya amince da nadin Injiniya Umar Abdullahi Umar a matsayin babban darektan ayyuka a hukumar REA
  • Wannan na zuwa ne bayan dakatar da shugaban hukumar, Ahmed Salihijo da wasu daraktocin hudu kan badakalar kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba Umar Abdullahi Ganduje babban mukami a hukumar samar da wuta a ƙauyuka (REA).

Tinubu ya nada Umar wanda ɗa ne ga shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje babban darektan ayyuka na hukumar.

Tinubu ya sakawa ɗan Ganduje da babban mukami a hukumar REA
Bola Tinubu ya naɗa Umar Ganduje a REA Hoto: Bola Tinubu, Umar Abdullahi Umar.
Asali: Facebook

Gwagwarmayar Abba Ganduje a zaben 2023

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

Sabon darektan hukumar, Injiniya Ganduje ya shiga siyasar 2023 tsundum inda ya nemi takarar majalisar tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nemi takarar mazabar bayan mahaifinsa ya janye daga neman takarar sanata a jihar Kano.

Umar Abdullahi daga bisani ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado inda Hon. Tijjani Jobe na NNPP ya yi nasara.

Har ila yau, Umar ya taka rawar gani a yakin neman zaben Tinubu da Shettima a 2023 musamman bangaren matasa.

Dalilin nada Abba Ganduje mukamin

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Wannan nadin na Umar na zuwa ne bayan dakatar da shugaban hukumar, Ahmed Salihijo kan zargin badakalar kudade.

Salihijo wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi a 2019 an dakatar da shi da wasu darektocin hukumar uku.

Kara karanta wannan

Ban taba ganin irinsa ba, Hadimin Tinubu ya fadi lokacin da Tinubu ke kwanciya duk daren Allah

Darektocin da aka sallaman sun hada da Olaniyi Alaba Netufo da Barka Sajou sai kuma Sa’adatu Balgore.

Yayin da Tinubu ya nada Aliyu Abubakar wanda ya maye gurbin Salihijo ya kuma naɗa sababbin darektoci uku ciki har da ɗan Ganduje.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Ganduje

Kun ji cewa, Babbar kotun tarayya mai zama a birnin Kano ta yanke hukunci kan bidiyon dala na Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun ta yanke hukuncin cewa hukumar PCACC ba ta da hurumin bincikar Ganduje kan bidiyon zargin karbar cin hancin dala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.