Duniya Ta Yi Attajirin da Ya Fi Kowa Kudi Bayan Doke Elon Musk, Dangote Ya Kara Arziki

Duniya Ta Yi Attajirin da Ya Fi Kowa Kudi Bayan Doke Elon Musk, Dangote Ya Kara Arziki

  • Elon Musk ya rasa matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya sannan kuma ya yi asarar Naira tiriliyan 1.6 na dukiyarsa
  • Jeff Bezos yanzu yana riƙe da kambun a matsayin wanda ya fi kowa arziƙi a duniya, a cewar wata ƙididdigar Bloomberg
  • Attajirin nan na Afrika, Aliko Dangote ya samu sama da dala miliyan 140 (sama da N215bn) a cikin sa’o’i 24 da suka wuce

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jeff Bezos, shugaban kamfanin Amazon, ya sake karɓe kambunsa a matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a duniya, inda ya mallaki dalar Amurka biliyan 200.

Lokaci na ƙarshe da Bezos ya kasance mafi arziƙi a duniya shine a cikin shekarar 2021.

Arzikin Dangote ya karu
Jeff Bezos ya doke Elon Musk a jerin attajiran duniya Hoto: Chesnot
Asali: Getty Images

Yadda Bezos ya zama mai arziƙin duniya

Kara karanta wannan

Matashin mai adaidaita sahu da ya mayar da N15m ya sake samun gagarumar kyauta, bayanai sun fito

Bezos ya sake karɓar kambun ne bayan hannun jarin kamfanin Amazon ya yi tashin gwauron zabi, cewar Google Finance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu hannun jarin kamfanin ya haɓaka da kaso 17% wanda hakan ke nuna ƙarin kusan kaso 90% fiye da shekarar da ta gabata.

Bezos ya mallaki kusan kaso 9% na Amazon, babban wurin sayan kayayyaki a yanar gizo na duniya. Dukiyarsa na ƙaruwa lokacin da hannun jarin Amazon ya tashi.

Bayanai daga ƙididdigar attajirai wacce Bloomberg ta yi, sun nuna cewa ƙaruwar darajar hannun jarin kamfanin ya sanya Bezos ya samu dala biliyan 23.4 a shekarar 2024.

Elon Musk ya koma na biyu

Elon Musk, shugaban Twitter da Tesla, a halin yanzu shi ne na biyu a jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya, inda yake da dukiyar da ta kai dala biliyan 198 ya zuwa ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano ya ba 'yan kasuwa muhimmiyar shawara kan azumin watan Ramadan

A ranar Litinin kaɗai arziƙin Musk ya ragu da dala biliyan 17.6 kuma ya zuwa yanzu ya yi asarar dala biliyan 31.3 na dukiyarsa.

Na kusa da shi a cikin jerin hamshaƙan attajirai akwai hamshaƙin attajirin nan ɗan ƙasar Faransa, Bernard Arnault, wanda ke da arziƙin da ya kai dala biliyan 197.

Mark Zuckerberg da Bill Gates sun kammala jerin sunayen manyan attajirai biyar na duniya da dala biliyan 179 da dala biliyan 150, bi da bi.

Dangote ya ƙara yin sama

Har ila yau, attajirin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya, Aliko Dangote, arziƙinsa ya ƙaru da dala miliyan 141 a cikin sa’o’i 24 zuwa dala biliyan 14.8 a ranar 5 ga watan Maris.

Dangote a halin yanzu yana matsayi na 132 a jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya, inda ya ƙara yin sama da matsayi huɗu idan aka kwatanta da matsayinsa na 136 a farkon watan Maris 2024.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Sama da 90% na ainihin masu aƙidar ta'addanci sun mutu Inji Zulum

Dukiyar Dangote Ta Ragu Kwanaki

A wani labarin kuma, kun ji cewa arziƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ragu sosai.

Hamshaƙin attajirin ya yi asarar kimanin dala biliyan uku a cikin mako ɗaya bayan darajar naira ta faɗi ƙasa warwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng