Matashin Mai Adaidaita Sahu da Ya Mayar da N15m Ya Sake Samun Gagarumar Kyauta, Bayanai Sun Fito

Matashin Mai Adaidaita Sahu da Ya Mayar da N15m Ya Sake Samun Gagarumar Kyauta, Bayanai Sun Fito

  • Halin kirki da gaskiyar da Auwalu Salisu ya nuna na ci gaba da bibiyarsa inda yake samun kyaututtuka masu gwaɓi
  • Matashin mai adaidaita sahun wanda ya mayar da N15m da aka manta a kekensa, ya samu tallafin yin karatu har zuwa matakin digirin digir
  • Bayan samun tallafin karatun an kuma ba shi lambar yabo ta gwarzon matashin shekarar 2023 saboda gaskiyar da ya nuna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Auwalu Salisu matashin nan mai shekara 23 a Kano, wanda ya mayar da maƙudan kuɗi Naira miliyan 15 da wani ɗan ƙasar Chadi ya manta a adaidaita sahunsa a shekarar 2023, ya samu tallafin yin karatu.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Matashin mai adaidaita sahun ya samu tallafin yin karatu har zuwa matakin digiri na uku watau digirin digir, wanda kuɗin za su kai N250m, cewar rahoton jaridar Leadership.

Awwalu Salisu ya samu tallafin karatu
An ba Awwalu Salisu tallafin karatu har zuwa matakin digirin digir Hoto: @imranmuhdz
Asali: Twitter

Auwalu ya samu wannan tallafin ne a wajen karrama shi da kamfanin 'Leadership Media Group' ya yi, a wajen bikin bayar da lambobin yabo na shekara-shekara da ya saba yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen bikin kamfanin ya ba matashin lambar yabo ta 'Gwarzon matashin shekarar 2023' saboda tsantsar gaskiyar da ya nuna.

Su waye suka ba Auwalu tallafin karatu?

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, shi ne ya fara ba Auwalu gurbin karatu a jami'ar Baze da ke Abuja har zuwa matakin digirin digir.

A wajen taron an karrama Peter Obi da matashin 'Gwarzon ɗan siyasar shekarar 2023'.

Bayan haka, gwamnan jihar Neja, kuma wanda ya lashe kyautar 'Gwarzon Gwamna na shekarar 2023', Mohammed Umar Bago, ya mayar da martani cikin raha yana mai cewa ba za a bari jam’iyyar LP ta zarce jam’iyyar APC mai mulki ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

A sakamakon haka Bago ya sanar da kyautar tallafin karatu har na N250m ga Awwalu don jin daɗin aikinsa na gaskiya da kuma ƙarfafa gwiwar sauran matasan Najeriya don nuna halin kirki.

Ya ce Auwalu zai samu tallafin N50m daga gare shi, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ministocinsa, ƙungiyar gwamnonin APC da kuma gwamnatin jihar Neja.

Bago ya ƙara da cewa zai sanya sunan Auwalu a ɗaya daga cikin ayyukan tituna da yake gudanarwa a jihar Neja.

Majalisa Ta Ba Auwalu Kyauta

A baya rahoto ya zo cewa matashin mai adaidaita sahu da ya mayar da N15m da aƙa manta a kekensa a Kano, ya samu kyauta daga majalisar dokokin jihar.

Majalisar dokokin ta ba Auwalu Salisu kyautar zunzurutun kuɗi har N1.5m domin halin gaskiya da gudun haramun da ya nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng