Digiri Kan Hisbah: Daurawa Ya Lissafa Abubuwa 3 Da Za Su Yi a Inganta Aikinsu a Kano

Digiri Kan Hisbah: Daurawa Ya Lissafa Abubuwa 3 Da Za Su Yi a Inganta Aikinsu a Kano

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Bayan kalubalantar ayyukan 'yan Hisbah da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi, shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu matakai da za su dauka.

Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya dawo kan kujerarsa bayan murabus da ya yi ya ce za su duba inda kuskure yake a aikinsu domin su gyara.

Malam Daurawa ya ce za su inganta ayyukan Hisbah
Aminu Daurawa ya ce za su inganta ayyukan Hisbah a Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Youtube

A cewarsa, duk wani aiki ko ma'aikata ta gaji yin kuskure yana mai nuni ga abin da ya faru da rundunar soji, inda ta yi kuskuren sakin bam kan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba.

A hira da ya yi da BBC Hausa, malamin ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane matsorata ne, sun cancanci hukuncin kisa, Remi Tinubu ta magantu a bidiyo

“Dama aiki abin da ake so a ci gaba da inganta shi, in shaa Allahu yanzu za mu dauki matakai guda hudu domin a kara inganta aikin."

Legit Hausa ta tattauro wasu jerin matakai uku da Shehin malamin ya ce za su yi amfani da su wajen inganta ayyukan Hisbah. Ga su nan a kasa:

1. Horar da jami'an Hisbah

Shugaban hukumar ta Hisbah reshen Kano ya bayyana cewa daga cikin kokarin da suke na inganta ayyukan 'yan Hisbah akwai horar da jami'ai, domin koyar da su yadda tsarin aikinsu yake.

“Za a horar da su kansu ma’aikatan, dukkan ma’aikatu da jami’ai dama ana samun irin wannan kuskuren, kwanan nan sojoji suka yi kuskure suka jefa bam, suka kone jama’a gaba daya."

- Aminu Daurawa

2. Karatun digiri da difloma kan aikin Hisbah

Har ila yau, Sheikh Daurawa ya sanar da shirin da hukumar Hisbah karkashin jagorancinsa take yi na kafa makarantar horar da 'yan Hisbah. Ya ce za su rika yin karatun difloma, NCE da ma digiri a makarantar.

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

“Sannan za mu yi kokari mu kafa makaranta mai suna “Makarantar horar da ‘yan Hisbah” wanda za a rika yin difloma, NCE har da digiri ma a kan aikin Hisbah sannan za mu kara inganta aikin ta bangaren ilimi da bangaren kwarewa," cewar Daurawa.

3. Samar da sassa da za su dunga bibiyar aikin Hisbah

Daga karshe, Shehin malamin ya bayyana cewa hukumar za ta samar da bangarori biyu na doka da fasahar sadarwar zamani domin bibiyar ayyukan 'yan Hisbah.

Haka kuma ya ce wadannan bangarori sune za su dunga bayar da shawarwari kan yadda hukumar za ta tafiyar da ayyukanta bisa doka da oda.

“Za mu yi sashen doka, sashen fasahar sadarwar zamani wanda za su rka taimaka mana wajen bibiyar ayyukan da suke faruwa da kuma bayar da shawarwari, da aikin doka da kuma bin doka da oda. In shaa Allahu Hisbah za ta ci gaba da aikinta dari bisa dari da doka da oda."

Kara karanta wannan

Minista: Dakarun sojoji sun hallaka manyan ƴan bindiga 7 da suka addabi mutane a Najeriya

- Aminu Daurawa

Legit Hausa ta tuntubi wasu mazauna garin Kano don jin ra'ayinsu game da wadannan yunkuri da Hisbah ke yi don inganta ayyukansu.

Malama Zainab ta ce:

"Lallai wannan abu da mallam yake son yi zai kawo ci gaba sosai a aikin Hisbah, zai sa a daina yiwa jami'an hukumar kallon kaskanci kuma zai kara karfafa ayyukansu."

Malam Shu'aibu Hassan ya ce:

"Yana da matukar alfanu a horar da jami'an Hisbah kan aikinsu domin hakan zai sa su dunga tafiyar da harkokinsu cikin kwarewa kuma bisa daidai. A nusar da su yadda ba za su dunga ketare iyaka ba.
"Sannan shirin bude wata makaranta ta musamman kan aikin ci gaba ne mai kyau, don hakan zai kara ba matasa karfin gwiwar shiga aikin."

Daurawa ya aika sako ga 'yan daudu da karuwai

A baya mun ji cewa Sheikh Daurawa ya ce sun ba duk wasu masu yada badala, kama daga 'yan daudu zuwa karuwai makonni biyu su tuba, sannan cewa za a basu kudi domin su ja jari tare da koya masu sana'a.

A wata hira da aka yi da shi, malamin ya gargadi wadanda basu da niyar tuba da su tattara su bar Kano domin jihar ba ta fasikai bace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng