Tallafin Man Fetur: Tsohon Gwamnan Arewa Ya Fallasa Tinubu, Ya Ce Har Gobe Ana Biyan Kudi

Tallafin Man Fetur: Tsohon Gwamnan Arewa Ya Fallasa Tinubu, Ya Ce Har Gobe Ana Biyan Kudi

  • Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya fallasa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu inda ya ce har yanzu ta na biyan tallafin man fetur
  • Idan ba a manta ba, a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai "saboda bai dace ba"
  • Yayin da ya ke goyon bayan janye tallafin, Yuguda ya yi nuni da cewa Tinubu ya cire tallafin da ke shiga aljihun wasu tsirarun mutane ne kawai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya ce har yanzu gwamnatin tarayya na biyan tallafin man fetur.

Yuguda ya bayyana haka ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels a shirinsu na siyasa na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

PDP ta samu baki yayin da gwamnanta a Arewa ya dira kan Buhari, ya fadi illar da ya yi wa Najeriya

Tallafin man fetur
Har yanzu Tinubu na biyan tallafin fetur, in ji Yuguda. Hoto: @officialABAT (X), Getty Images
Asali: Facebook

Fetur: Hukumar IMF ta zargi Tinubu da biyan tallafi

Idan ba a manta ba, Legit ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, ya bayyana cewa, “na janye tallafin mai.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya kara da cewa kasafin kudin shekarar 2023 bai dauke da tallafin man fetur, haka kuma, biyan tallafin da kasar ke yi bai dace ba.

Sai dai wani rahoton Legit na baya-bayan nan ya nuna cewa 'hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF)' ta zargi gwanatin tarayya da ci gaba da biyan tallafin fetur din.

Yadda ake karkatar da tallafin man fetur - Yuguda

Da yake magana kan batun tallafin, Yuguda ya ce:

"Idan IMF ta ce har yanzu Najeriya na biyan tallafi to da gaske ne muna biya, domin tallafin da aka cire shi ne wanda ke shiga aljihunan wasu tsirarun mutane.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

"Ya kamata mutane su fahimta, ba gaba daya ne gwamnati ta daina biyan tallafin ba, amma ta daina biyan wanda ke zamarwa kasar illa ta fuskar tattalin arziki."

- Isa Yuguda

Yuguda ya yi nuni da cewa tun farko bai goyi bayan kudin da ake narkawa a tallafin fetur din ba, a cewarsa, wasu tsiraru ne kawai ke arziki da hakan.

Amfanin daina biyan tallafin fetur - Yuguda

Tsohon gwamnan jihar Bauchin, ya kuma ce:

"Kudaden da yanzu jihohi ke samu daga kasafin wata-wata ya nunnuka na baya sau biyu ko uku, kuma wannan ya faru sakamakon daina biyan tallafin fetur din.
"Muna sane da yadda aka rinka fitar da kudi da sunan biyan tallafin mai da ake hakowa, alhalin babu wadannan rijiyoyin man, kawai a takarda suke."

- Isa Yuguda

Talaka ya kara hakuri, Najeriya za ta saitu - Yuguda

Vanguard ta ruwaito Isa Yuguda ya na tsokaci kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar, inda ya yi nuni da cewa, 'yan Najeriya ba za su fahimci kokarin Tinubu na dawo da tattalin arziki ba har sai ya cimma gaci.

Kara karanta wannan

'Dan gida ya fasa kwai, ya jefi Gwamnatin Tinubu da biyewa manufofin turawa

Yuguda ya ce akwai bukatar mukarraban gwamnatin shugaban kasar su taimaka wajen wayar da kan talakawa yadda manufofin gwamnati za su sauya al'umma na gaba.

Alakar gwamnati da NNPCL wajen cire tallafin mai

Tun da fari, Legit ta ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya na amfani da kamfanin man fetur na kasa NNPCL wajen daidaita farashin fetur tare da hana shi tashi a kasuwar.

Wannan matakin a mahangar masu bincike na nuni da cewa har yanzu gwamnatin Najeriya na biyan tallafin fetur a boye duk da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.