Wata Mai POS Ta Shiga Hannu Kan Raba Jabun Kudade, Bidiyo Ya Bayyana

Wata Mai POS Ta Shiga Hannu Kan Raba Jabun Kudade, Bidiyo Ya Bayyana

  • Jami'an 'yan sanda sun kama wasu ma'aurata, Olamilekan da Oluwayemisi Oludare kan zargin raba jabun kudade
  • Olamilekan ya ce suna siyarwa 'yan canji da jabun kudaden waje yayin da matarsa ke rabawa kwastamoni jabun naira ta san'ar POS
  • Adeniyi Quadri mai shekaru 35 ya amsa laifinsa na bugawa Olamilekan jabun kudade kan N50,000

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - 'Yan sanda sun kama wata mata mai shekaru 46, Oluwayemisi Oludare kan zargin raba jabun kuddade, ta hanyar sana'ar POS a jihar Legas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Oluwayemisi ta bayyana cewa ta samu jabun kudaden ne daga wajen mijintam Olamilekan don rabawa a cikin kasuwar Oluwole da ke Legas.

Kara karanta wannan

'Yar bautar kasa ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max da ta kai miliyan 1.3, ta mayarwa mai ita

'Yan sanda sun kama mai POS da ke yada jabun kudade
Wata Mai POS Ta Shiga Hannu Kan Raba Jabun Kudade, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar Zone 2 da ke Onikan, Legas ne suka kama ma'auratan tare da wani kanal mai ritaya, Ilelabayo Johnson, da Adeniyi Quadri mai shekaru 35.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa wadanda ake zargin suna rabawa 'yan canji a Najeriya da Kamaru jabun kudade da kuma ta hanyar POS a Najeriya.

Muna siyarwa 'yan canji da jabun kudade, mai laifi

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Olamilekan ya amsa laifin cewa shine mamallakin jabun kudade naira miliyan 9 da 'yan sanda suka gano a wajensu.

Olamilekan ya ce:

"Muna siyar da wasu daga cikin jabun kudaden wajen ga 'yan canji yayin da matata wacce ke da wurin yin POS take bayar da jabun kudade ga kwastamomi."

Me rundunar 'yan sanda ta ce?

Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, AIG Olatoye Durosinmi, ya shaida wa manema labarai cewa, sashen sa ido na shiyyar sun kai samame mabuyar Quadri inda aka samu jabun CFA miliyan dari uku da naira miliyan tara, a hannunsa.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu galaba, sun halaka ƴan bindiga da yawa a jihohi 3 na Arewa

Durosinmi ya kara da cewa amsa laifinsu da ma’auratan suka yi ne ya kai ga kama tsohon jami’in sojan tare da kwato jabun kudade na gida da na waje a hannunsa.

Da yake amsa tambayoyi, Quadri ya ce:

"Ana biyana N10,000 don buga jabun kudade na N1,000 guda 1000. Tuni na buga kimanin naira miliyan 9 kafin a kama ni. An biya ni N50,000 don yin aikin.
"Olamilekan Oludare, ne ya koya mani sana'ar kimanin shekaru biyar da suka wuce. Yana zuwa wajena sau hudu a shekara."

CBN ya yi gargadi kan jabun kudade

A wani labarin, mun kawo a baya cewa yayin da ake fama da karancin kudi a Najeriya, Babban Bankin kasar ta gargadi yan Najeriya a kan jabun kudade da ke yawo.

Babban bankin kasar ya yi gargadin ne a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba mai taken "ku yi hattara da jabun kudi da ke yawo".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng