Hukumar NSC Ta Dakatar da Siyar da Kayan Abinci Kan Farashi Mai Rahusa, Ta Faɗi Dalili 1 Tak

Hukumar NSC Ta Dakatar da Siyar da Kayan Abinci Kan Farashi Mai Rahusa, Ta Faɗi Dalili 1 Tak

  • Hukumar kwastam ta ƙasa ta dakatar da aikin siyar da buhunan shinkafa da sauran kayan abinci a farashi mai rahusa ga ƴan Najeriya
  • Mai magana da yawun NCS ta kasa, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan turmutsitsin da jama'a suka yi a wurin siyar da kayan wanda ya yi ajalin rayuka da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta dakatar da siyar kayan abincin da ta kwace kan farashi mai rahusa.

Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne saboda turmutsitsin da aka yi wanda ya laƙume rayukan bayin Allah a tsohuwar hedkwatar kwastam da ke Aba.

Kara karanta wannan

Babban labari: Tinubu ya shirya amfani da rahoton Oronsaye, zai yi wani babban sauyi a Najeriya

An dakatar da sayar da kayan abincin da kwastam ta kwace.
Hukumar NSC Ta Dakatar da Siyar da Kayan Abinci Kan Farashi Mai Rahusa, Ta Faɗi Dalili 1 Tak Hoto: NCS
Asali: Twitter

Mai magana da yawun NSC na kasa, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 20 ga Fabrairu, 2024 ne Hukumar Kwastam ta ce za ta fito da kayayyakin abincin da ta kama domin rage wahalhalu da tsadar rayuwa da ake fama a kasar nan.

Me ya kawo tsaiko da sayar da shinkafar kwastam?

A karon farko dai Kwastam ta fito da kayan abinci a ofishinta na Aba, jihar Legas ranar Juma’ar da ta gabata a gaban sauran jami’an tsaro kamar ‘yan sandan Najeriya.

Maiwada ya ce:

"An fara fito da kayan abincin da misalin ƙarfe 8:00 na safiya kuma mun ji daɗin yadda jama'a suka bamu haɗin kai, aka riƙa fifita dattawa, masu naƙasa, mata masu juna biyu da sauran marasa ƙarfi."

Kara karanta wannan

"A shigo da abinci" TUC ta gano hanya 1 da zata share hawayen talakawa, ta aike da saƙo ga Tinubu

"Sai dai wani kalubale da bamu yi tsammani ba ya taso bayan mun gama aikin ranar farko kuma muka sanar cewa za a ci gaba washe gari. Daha nan ne mutane suka fara nuna ƙosawa.
"Aka fara turereniya wasu suka rika shiga kwantena kwantena da babu komai suna neman shinkafa, garin haka ne wasu suka ji rauni har da rasa rayuka."

Hukumar Kwastam ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari, kamar yadda The Nation ta rahoto.

TUC ta hango maganin damuwar ƴan Najeriya

A wani rahoton kuma Ƙungiyar kwadago TUC ta ƙasa ta bayyana abinda take ganin shi ne mafita a Najeriya yayin da ake fama da tsadar kayan abinci.

Yayin hira da ƴan jarida, shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya bukaci Bola Tinubu ya bada damar shigo da abinci daga ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262