Abubuwa 8 da Ya Kamata Ku Sani Game da Rahoton Oronsaye

Abubuwa 8 da Ya Kamata Ku Sani Game da Rahoton Oronsaye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye wanda ya ba da shawarar kafa gwamnati mai sassaucin ra'ayi.

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da aiwatar da rahoton a wani zama da shugaban ya jagoranta a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a Aso Rock, Abuja.

Tinubu zai aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye
Tinubu zai aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye na sake fasalin ma'aikatu da hukumomi. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

Ga jerin abubuwa takwas da ya kamata ku sani game da rahoton:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kafa kwamitin Stephen Oronsaye a 2011

Kara karanta wannan

Babban labari: Tinubu ya shirya amfani da rahoton Oronsaye, zai yi wani babban sauyi a Najeriya

A shekarar 2011 ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin kasa da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Stephen Oronsaye.

2. Jerin mambobin kwamitin

Kwamitin shugaban kasa ya kunshi mambobi kamar haka; Stephen Oronsaye (shugaba); Japh CT Nwosu (mamba) da Rabiu D. Abubakar (mamba).

Sauran mambobin kwamitin su ne; N. Salman Mann, Hamza A. Tahir, Adetunji Adesunkanmi, Member da Umar A. Mohammed.

3. Kwamitin ya mika rahoto a 2012

Kwamitin ya gabatar da rahoto mai shafuka 800 a ranar 16 ga Afrilu, 2012, inda ya bankado yadda ake gudanar da gasa a tsakanin hukumomi da dama.

4. Rahoton ya bankado almubazzaranci

Wannan ba wai kawai ya haifar da rashin jin dadi a tsakanin hukumomin gwamnati ba, har ma ya bankado da irin almubazzarancin da ake yi wajen tafiyar da hukumomin.

5. Dakatar da ba hukumomi da cibiyoyi kudi

Har ila yau, ya ba da shawarar dakatar da fitar da kudaden da gwamnati ke ba wa wasu hukumomi da cibiyoyi don kara yawan kudin da za a gudanar da manyan ayyuka.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamishinan NPC, ya shiga muhimmin taro da jiga-jigai a Villa

6. Adadin yawan hukumomi da ma'aikatun gwamnati

Rahoton na Oronsaye ya tabbatar da cewa akwai hukumomin gwamnatin tarayya 541, kwamitoci da hukumomi (na doka da kuma wadanda ba na doka ba).

7. Shawarar da Stephen Oronsaye ya ba gwamnati

Ya ba da shawarar rage yawan hukumomin gwamnati daga 263 zuwa 161, yayin da ya nemi a rushe hukumomi 38 sannan a hade guda 52.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa a mayar da hukumomi 14 su koma sassa na ma'aikatu, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

8. Abin da gwamnati ta yi kan rahoton

Daga baya gwamnati ta kafa kwamiti karkashin jagorancin babban lauyan gwamnatin tarayya na wancan lokaci, Mohammed Adoke SAN, domin nazarin shawarwarin da kuma fitar da abubuwan aiwatarwa daga rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.