Tsadar Rayuwa: Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) Sun Bukaci a Yi Musu Karin Alawus, Sun Fadi Dalili
- Halin matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasa ya sanya masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) aikewa da wasiƙa zuwa ga Shugaba Tinubu
- Masu hidimtawa ƙasar sun koka kan halin ƙaƙanikayi da suka tsinci kansu a ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki
- Sun buƙaci shugaban ƙasan da ya yi musu ƙarin kuɗaden alawus da ake ba su duk ƙarshen wata domin a yanzu N33,000 ta yi musu kaɗan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu daga cikin masu yi wa ƙasa hidima sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya waiwaye su domin ƙara kuɗin alawus-alawus da ake biyansu a jihohi 36 na ƙasar nan.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da suka koka kan yadda tsadar kayan masarufi da tsadar rayuwa ta tilasta musu yin ƴan ƙananan ayyuka domin tsira da mutuncinsu.
Jaridar The Punch ta ce masu yi wa ƙasa hidimar sun bayyana hakan ne a wata wasiƙa ƙarƙashin ƙungiyar 'Concerned Corp Members’ da suka aike wa shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun koka da cewa alawus din N33,000 da ake ba su a duk ƙarshen wata ya yi musu kaɗan duba da matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan.
Jaridar Vanguard ta ce ko a baya masu yi wa ƙasa hidimar sun buƙaci da ayi musu ƙarin alawus, bayan an ƙara albashin ma'aikata.
Menene ƙorafin masu yi ƙasa hidimar?
Sun yi nuni da cewa hakan ya sanya su neman da a yi musu ƙari domin rage musu raɗaɗin da suke ciki.
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:
"Hauhawar farashin kayyaki a kasuwanni ya ƙara samu cikin matsala. Wasu abubuwan buƙata sun zama abin da ba za su samu ba, wanda hakan ya jefa da yawa daga cikinmu cikin halin ƙaƙanikayi.
"A dalilin hakan da yawa daga cikinmu sun koma ɗebowa da amfani da ruwan rafi domin sha, sannan wasu har gona suke zuwa su yi aiki domin a ba su abinci.
"Waɗannan abubuwan sun jefa rayukanmu cikin hatsari da yanayi mara kyau wanda zai cutar da mu nan bada jimawa ba ko nan gaba.
Hukumar NYSC ta yi martani
Da aka tuntuɓi daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na hukumar NYSC, Eddy Megwa, ya ce za a duba koken masu yi wa ƙasa hidimar.
Ya yi nuni da cewa akwai tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi la’akari da masu yi wa ƙasa hidimar a yunƙurin da take na rage wahalar da jama'a ke fuskanta.
A kalamansa:
"Ba aikin hukumar NYSC ba ne ƙara alawus-alawus ga masu yi wa ƙasa hidima, aikin gwamnatin tarayya ne. Ganin cewa wannan gwamnati mai son matasa ce, tabbas za ta yi wani abu game da alawus-alawus ɗinsu idan aka tashi duba albashin ma’aikatan gwamnati."
An Yi Wa Ƴan NYSC Ƙarin Kuɗin Alawus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya yi wa masu yi wa ƙasa hidima ƙarin kuɗaɗen alawus a jihar.
Gwamnan ya sanar da ƙarin kaso 100% na kuɗaɗen alawus da gwamnatin jihar ke ba masu hidimtawa ƙasa a jihar.
Asali: Legit.ng