'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Ƙashe Babban Dan Sanda Yana Tsaka da Aiki a Jihar PDP
- Ƴan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun bude wa tawagar jami'an ƴan sanda wuta yayin da suke bakin aiki a shingen bincike a jihar Ribas
- Yayin wannan farmaki, babban jami'an ɗan sanda da ya kai matakin insufekta ya rasa rayuwarsa, sannan jami'an sun sheƙe ɗaya daga cikin ƴan bindigar
- Kwamishinan yan sandan jihar Ribas ya jaddada cewa dukkan masu kai farmaki kan ƴan sanda da sauran ƴan ƙasa zasu ɗanɗana kuɗarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ribas ta bayyana cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun kashe Insufekta yayin wani harin kwantan ɓauna.
Maharan sun kashe babban jami'in ɗan sandan ne yayin suka yi wa jami'ai kwantan ɓauta a shingen binciken gadar sama Eliozu a ƙaramar hukumar Obio/Akpo.
Mai magana yawun rundunar ƴan sandan Ribas, Grace Iringe-Koko, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iringe-Koko ta ce ‘yan bindigar a cikin wata motar bas Sienna, sun taso ne daga mashigar Rumuodumaya, kusa da Fatakwal inda suka kai farmakin da ya yi ajalin Insufektan.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka"
Ta kuma ƙara da cewa nan take tawagar ƴan sanda suka kai ɗauki wurin kuma suka kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigar wanda ya sa hular ɓoye fuska.
A cewarta, sauran ƴan bindigan sun arce domin tsira yayin da dakarun ƴan sanda suka buɗe musu wuta ba kaƙƙautawa.
Kakakin ƴan sandan ta ce:
"Muna matuƙar takaicin sanar da mummunan harin da aka kai wa ƴan sandan sashin Operation Sting na rundunar ƴan sandan jihar Ribas ranar 21 ga watan Fabrairu.
"Wasu ƴan bindiga a motar Sienna mai baƙin gilashi sun kai harin kwantan ɓauna kan jami'an ƴan sanda yayin da suke aikin binciken ababen hawa a gadar sama ta Eliozu.
"Daga zuwan ƴan bindigar suka bude wa tawagar ƴan sandan wuta wanda ya yi sanadin mutuwar Insufekta, wanda ya rasa ransa a bakin aiki.
Su wa suka kai wannan farmaki?
Rundunar ƴan sanda ta gudanar da cikakken bincike kan wannan danyen aikin kuma tuni ta gano kungiyar da ta kai wannan hari, rahoton Vanguard.
Kwamishinan ‘yan sanda, Olatunji Disu, ya sake nanata cewa babu shakka dukkan masu cin zarafin ‘yan sanda ko wani dan kasa za su fuskanci fushin doka.
Jirgin ruwa ya gamu da haɗari a Legas
A wani rahoton kuma An rasa mutum ɗaya yayin wani jirgin ruwa na fasinja ya gamu da hatsari a yankin Ikoyi ta jihar Legas ranar Laraba da yamma.
Kakakin hukumar kula da hanyoyin ruwa na jihar, Wuraola Alake, ya ce an ceto mutum 15 daga cikin fasinjoji 17 da jirgin ya kwaso.
Asali: Legit.ng