Innalillahi: Jirgi Maƙare da Mutane Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar APC, Rai Ya Salwanta
- An rasa mutum ɗaya yayin wani jirgin ruwa na fasinja ya gamu da hatsari a yankin Ikoyi ta jihar Legas ranar Laraba da yamma
- Kakakin hukumar kula da hanyoyin ruwa na jihar, Wuraola Alake, ya ce an ceto mutum 15 daga cikin fasinjoji 17 da jirgin ya kwaso
- Ya bayyana cewa har kawo yanzu jami'ai na can suna aikin ceto a wurin da lamarin ya faru, ragowar fasinja ɗaya ya ɓata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Legas - Wani jirgin ruwa da ya ɗauko fasinjoji 17 ya gamu mummunan hatsari a yankin Ikoyi da ke jihar Legas ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.
A rahoton da Channels tv ta tattara, haɗarin jirgin ya yi ajalin mutum ɗaya yayin da sauran kuma aka yi nasarar ceto rayuwarsu.
Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4
Hadarin ya afku ne a lokacin da jirgin ruwan ya yi karo da wani kankare na siminti a bakin teku a daidai wurin da ake gina layin wutar lantarki a gadar Lekki-Ikoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasinjoji 15 sun tsallake rijiya da baya
Mai magana da yawun hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas, (LASWA), Wuraola Alake, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa an yi nasarar ceto fasinjoji 15 daga cikin ruwan jim kaɗan bayan faruwar hatsarin da misalin ƙarfe 6:50 na yammacin ranar Laraba.
Alake, wanda ya tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, ya bayyana cewa har yanzun ba a gano ragowar mutum ɗaya ba.
Me ya jawo haɗarin jirgin?
Ya ce:
"Da misalin ƙarfe 6:50 na yammacin yau Laraba, wani jirgin ruwan haya mai suna T-Ben, wanda ya taso daga Addax jetty, ya ci karo da kankare a wurin da ake gina hanyar wutar lantarki a gadar Lekki zuwa Ikoyi.
"An ceto 15 daga cikin fasinjoji 17 da ke cikin jirgin ruwan yayin da mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa, har yanzu da muke wannan sanarwan ana ci gaba da aikin lalube.
"Jami'an sashin bincike da ceto na hukumar LASWA, masu jiragen haya da sauran ƴan sa kai na ci gaba da aikin ceto a wurin da lamarin ya afku."
Mutanen Legas za su samu sauƙin rayuwa
A wani rahoton kuma Babajide Sanwo-Olu ya sanar da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin rage wa mazauna jihar Legas raɗaɗin halin matsin da aka shiga.
Gwamnan ya bayyana rage wa ma'aikata ranakun aiki daga kwanaki 5 zuwa 3, yayin da malamai kuma za a ba su alawus na hawa mota.
Asali: Legit.ng