Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci a Hukumar ‘Immigration’ Ta Najeriya
- Shugaba Tinubu ya nada DCG Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS)
- DCG Nandap za ta karbi ragamar mulki daga hannun Wura-Ola Adepoju, wadda wa'adin aikinta ke karewa a ranar 29 ga Fabrairu, 2024
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DCG Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS).
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa , ya ce nadin zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2024.
Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shafukan sada zumunta ne ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, nada DCG Nandap ya yi daidai da "sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke yi a cikin ayyukan hukumar".
Ngelale ya ce:
“DCG Nandap za ta karbi ragamar hukumar daga hannun Misis Caroline Wura-Ola Adepoju, wacce wa’adinta zai kare a ranar 29 ga Fabrairu, 2024.
“Kafin nadin ta a matsayin Kwanturola-Janar, Nandap ta kasance mataimakiyar Kwanturola-Janar mai kula da bangaren hijira na hukumar."
Shugaban ya yi hasashen cewa sabuwar shugabar za ta karfafa gyare-gyaren da ake yi a hukumar tare da samar da ingantacciyar hanyar isar da aiki mai inganci ga ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng