Tinubu Ya Sake Korar Wani da Buhari Ya Nada, Ya Sanar da Wace Zata Maye Gurbinsa

Tinubu Ya Sake Korar Wani da Buhari Ya Nada, Ya Sanar da Wace Zata Maye Gurbinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya zabi Hafsat Abubakar Bakari a matsayin sabon shugaban hukumar da ke Hukumar da ke tattara bayanai a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci
  • Nadin Bakara na nufin kai tsaye an kori Moddibo Hamman-Tukur, wanda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada a 2019
  • Wannan shine nadi na biyu da Shugaba Bola Tinubu ya yi tun bayan dawowarsa kasar daga Addis Ababa a ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Fadar Shugaban Kasa - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami Moddibo Hamman-Tukur a matsayin shugaban Hukumar da ke tattara bayanai a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci (NFIU).

Shugaban kasar ya kuma nada Ms Hafsat Abubakar Bakari a matsayin wacce za ta maye gurbinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya fadi matakin da ya kamata 'yan Najeriya su 'dauka kan mulkin Tinubu

Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban NFIU
Tinubu ya maye gurbin Modibbo da Hafsat a matsayin shugaban NFIU. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya magantu kan sabuwar wacce ya nada

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, wanda ya sanar da nadin, ya ce majalisar tarayya ce za ta tabbatar da nadin.

Sanarwar ta ce:

"Kafin nadinta a matsayin shugaban na NFIU, ta yi aiki a matsayin direkta a NFIU, kuma a lokuta daban-daban ta rike shugaban sashin ayyuka; shugaban tsare-tsare da wayar da kai, da shugaban majalisar sakatariyar hukumar yaki da rashawa (EFCC).
"Shugaban kasar yana sa ran Ms. Bakare za ta kawo kwarewarta domin gudanar da wannan muhimmin aikin, musamman bisa yakin da gwamnatinsa ke yi da shigo da kudin haram da wasu ayyukan ba dai-dai ba da suka yi katutu a kasuwar canji."

Tinubu ya nada tsohon shugaban NYSC

Wannan nadin shine na biyu da Tinubu ya yi tun bayan dawowarsa daga taron Kungiyar Hadin Kan Afirka a Addis Ababa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sabon nadi mai muhimmanci a hukumar ‘Immigration’ ta Najeriya

Tunda farko, Shugaban kasar ya nada Manjo Janar Suleiman Kazaure (mai murabus), tsohon shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) don ya jagoranci sabuwar kwamiti ta musamman da aka kafa don kawar da munanan halaye a manyan makarantu (SESV-TI).

Babban mai taimakawa Shugaba Kasa Tinubu na musamman kan harkokin dalibai, Sunday Asefon, ya sanar da nadin a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164