Tinubu Ya Bada Umurnin Biyan Bashin Kudin Lantarki Na Gidan Gwamnati Don Kudi Kada a Yanke Wuta
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bada umurnin biyan naira miliyan 342 a matsayin bashin kudin lantarki ga Kamfanin Rarraba Wutan Lantarki na Abuja (AEDC) da ake bin gidan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Umurnin na shugaban kasa na zuwa ne bayan daidaita akawun tsakanin Gidan Gwamnati a Mahukunta na Hukumar AEDC.
A cewar sanarwa mai dauke da sa hannun Mashawarcin Tinubu na musamman kan Yada Labarai da Tsare-Tsare, Bayo Onanuga, a ranar Talata:
"Akasin ikirarin da AEDC ta yi da farko na bin bashin N932m a jaridu, bashin da ake bin Gidan Gwamnati N324.35m ne."
An yi wa sanarwar da lakabin 'Shugaba Tinubu ya bada umurnin biyan kudin lantarki na Gidan Gwamnati.'
Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya ba wa AEDC tabbacin cewa za a biya bashin kafin karshen wannan makon.
Dakaci karin bayani ...
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng