Murna Yayin da Gwamnan APC Ya Yi Wa Matasa 'Yan NYSC Karin Kaso 100% Na Alawus a Arewa
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya tausayawa matasa masu yi wa ƙasa hidima duba da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasa
- Gwamnan ya amince da yi wa matasan ƙarin kaso 100% na alawus ɗin da gwamnatin jihar ke ba ƴan NYSC da aka tura jihar
- Gwamnan dai ya ƙara alawus ɗin ne daga N5000 zuwa N10,00 domin ba matasan damar gudanar da aikinsu cikin sukuni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da ƙarin kaso 100% na alawus-alawus na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da aka tura jihar Sokoto.
Jaridar The Punch ta ce an ƙara alawus ɗin daga N5,000 zuwa N10,000 don hidimar ƙasa ta shekara ɗaya.
Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin buɗe sansanin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima na hadin gwiwa tsakanin jihohin Sokoto da Zamfara, na rukunin Batch '1' A a Farfaru jihar Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnan ya ƙara kuɗin alawus ɗin?
Gwamnan ya bayyana cewa:
"Na amince da hakan ne bisa la’akari da halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki da kuma muhimmancin da shirin NYSC ke da shi ga ci gaban ƙasa da jihar baki ɗaya.
"Na kuma bayar da kyautar Naira 10,000 ga kowane mai yi wa ƙasa hidima da aka tura zuwa jihohin Sokoto da Zamfara wanda a halin yanzu ake horaswa a matsayin kyautar maraba.
"Ina ba ku umarni da ku kasance masu kyawawan halaye kuma ku rungumi ruhin 'Najeriya ɗaya' kuma ku ɗauki dukkan ƴan ƙasa a matsayin ƴan Najeriya."
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga shirin domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Ministar Matasa Ta Magantu Kan Ƙara Alawus Ɗin NYSC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministar matasa, Jamila Bio Ibrahim, ta yi magana kan yiwuwar ƙarawa masu yi wa ƙasa hidima alawus.
Ministar ta bayyana cewa ba ta za iya bayar da tabbaci ba kan yin ƙarin saboda kuɗaɗen shiga na gwamnatin sun ragu.
Asali: Legit.ng