Zazzafar Muhawara Ta Ɓarke, Sanatoci Sun Fara Musayar Yawu a Majalisar Dattawa Kan Batun N29tr
- Muhawara mai dumi ta ɓarke a tsakanin mambobin majalisar dattawan Najeriya kan bashin kuɗi N29tr da gwamnati ta ci daga CBN
- Gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbi kuɗin daga babban bankin Najeriya CBN ta kashe su kuma har ta tafi ba ta biya bashin ba
- Tuni dai gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta lashi takobin bincikar abinda aka yi da kuɗin waɗanda ta zo ta taras
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa muhawara mai zafi ta ɓarke a zauren majalisar dattawan Najeriya kan bashin N29trn da tsohuwar gwamnati ta ciyo.
Sanatoci sun yi musayar yawu kan batun waɗannan maƙudan kuɗi waɗanda tsohuwar gwamnati karkashin Muhammadu Buhari ta karɓa daga babban banki CBN.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta yanke shawarar bin diddigin yadda aka ɓatar da kudin har N29tr.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta ce za ta gudanar da bincike a tsanake kan waɗannan kuɗi da tsohuwar gwamnati ta barta da aikin biya.
Legit Hausa ta fahimce cewa mambobin majalisar dattawan sun ci gaba da tafka muhawara kan makudan kudin bashin da ake kira 'Ways and Means'.
Yadda sanatoci suka yi musayar yawu a zauren majalisa
Yayin muhawarar, Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce majalisar dattawan ta tafka kuskure tun farko da ta yarda aka karɓo kuɗaɗen daga babban banki CBN.
Ndume ya ce:
"Lokacin da bukatar karɓo N22.7tr ta zo gaban majalisar dattawa ta 9, na tsaya kai da fata sai an mana cikakken bayani kafin mu amince amma aka yi banza da ni, majalisa ta amince."
A nasa tsokacin, Mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau, ya ce a lokacin an amince da bukatar da murya ɗaya tare da gargadin cewa ya kamata bangaren zartarwa ya kawo cikakken bayani daga baya, amma ba su kawo ba.
Da yake kare kansa, tsohon shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawal, ya ce duk wannan tada jijiyar wuyar kan kuɗi ne da aks riga an amince da su a baya.
Sai dai ya roki majalisar ta bar abinda ya wuce, ta maida hankali kan abubuwan da ke gabanta a yanzu.
A rahoton Punch, Lawal ya ce:
"Wannan duk ya riga ya wuce, abin da ya fi zama dole shi ne mu maida hankali kan halin da ake ciki, wanda kowa ya sani mutane na cikin yunwa kuma suna kuka."
Tinubu ya naɗa tsohon shugaban NYSC a muƙami
A wani rahoton kuma Jim kaɗan bayan ya dawo daga ƙasar Habasha, Bola Ahmed Tinubu, ya yi sabon naɗi da zai sauya akalar manyan makarantu a ƙasar nan.
Shugaban ƙasar ya naɗa tsohon darakta janar na NYSC, Suleiman Kazaure a matsayin shugaban kwamitin yaƙi da munanan ayyuka a manyan makarantu.
Asali: Legit.ng