Tsadar Rayuwa: Tsohon Gwamna Ya Goyi Bayan Tinubu, Ya Fadi Inda Matsalar Take

Tsadar Rayuwa: Tsohon Gwamna Ya Goyi Bayan Tinubu, Ya Fadi Inda Matsalar Take

  • Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel, ya ba ƴan Najeriya tabbaci a cikin taɓarɓarewar tattalin arziƙi
  • Ya jaddada muhimmancin haƙuri da fahimta, inda ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya gaji tattalin arziƙi wanda ke fuskantar ƙalubale
  • Sanatan ya gamsu da yunƙurin Tinubu na shawo kan waɗannan matsalolin, duk da cewa ba a cika magana a kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Sanatan Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, ya ja hankalin ƴan Najeriya da kada su yanke ƙauna kan tabarbarewar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya kuma jaddada buƙatar fahimtar juna, inda ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaji tattalin arziƙin da ke cike da matsaloli, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Emefiele: Akpabio ya fadi wani babban rudani da tsohon gwamnan CBN ya haifar

Gbenga Daniel ya ba 'yan Najeriya hakuri
Gbenga Daniel ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Tinubu Hoto: Otunba Gbenga Daniel
Asali: Facebook

Daniel ya nuna kyakkyawan fata, ganin cewa akwai yiwuwar samun ci gaba a nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ziyarar da ya kai ƙaramar hukumar Ijebu Ode a jihar Ogun, ya yi tsokaci ne kan matsalolin da ƙasar nan ke fama da su, inda ya danganta su da matsalolin tattalin arziƙin da Shugaba Bola Tinubu ya gada.

Tsohon gwamnan jihar Ogun ya amince da ƙoƙarin Tinubu na magance waɗannan matsalolin duk da cewa bai fito fili ya tattauna su ba.

Daniel ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi haƙuri da nuna goyon baya, yana mai jaddada ƙoƙarin gwamnati mai ci na inganta ci gaban ƙasa.

Kiran Gbenga Daniels ga ƴan Najeriya

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sanatan ya bayyana cewa:

"A gaskiya abubuwa ba za su yi kyau kamar yadda muke so ba amma ina so na roƙe ku jama’ata da ku nuna fahimta saboda shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu ya gaji abin da za mu iya kira gazawar tattalin arziƙi

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Buhari ya goyi bayan Sarkin Musulmi, ya gaya wa Tinubu abin da zai yi

"Amma ba zai yiwu ya yi magana ba. Duk abubuwan da suka faru a gabansa, ba zai iya yin magana ba, abin da yake ƙoƙarin yi shi ne neman mafita.
"Ina so in tabbatar muku da cewa sauƙi na nan tafe, kuma ƙasarmu za ta dawo daidai. Shugaban ƙasa yana buƙatar haɗin kan mu a yanzu fiye da kowane lokaci kuma ina tabbatar muku cewa nan ba da jimawa ba komai zai daidaita."

Ma'aikatan APC Na Shirin Yin Zanga-Zanga Kan Tsadar Rayuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatan da ke aiki a ɓangarori daban-daban a hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa, sun koka kan tsadar rayuwa.

Ma'aikatan sun yi barazanar cewa idan al'amura ba su daidaita ba, za su bi sahun masu fito tituna domin nuna rashin jindaɗinsu kan halin da ake ciki a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng