Ana Fama da Yunwa Ƴan Bindiga Sun Ƙona Kayan Abinci, Gidaje da Shanu, Sun Tafka Ɓarna a Arewa

Ana Fama da Yunwa Ƴan Bindiga Sun Ƙona Kayan Abinci, Gidaje da Shanu, Sun Tafka Ɓarna a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, sun tafka mummunar ɓarna ranar Lahadi
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun ƙona gidaje akalla 30 da kayan binci, kana suka yi awon gaba da mutane masu yawa
  • Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindigar sun kai hari garin ranar Jumu'a da ta gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Neja - Wasu miyagun ƴan bindiga sun tafka mummunar ɓarna yayin da suka kai farmaki ƙauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Yayin harin, ƴan bindigan sun ƙona gidajen al'umma aƙalla 30 tare da ƙona shanu masu ɗumbin yawa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace gawa da 'yan uwan mamacin, sun bukaci a ba su N50m

Yan bindiga sun kai hari jihar Neja.
Yan bindiga sun kona gidaje, kayan abinci da wasu muhimman abubuwa a jihar Neja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

An tattaro cewa kauyen Allawa na ɗaya daga cikin manyan garuruwan da ake noma mai kunshe da mutane akalla 2,000 a yankin Lakpama da ke ƙaramar hukumar Shiroro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban matasan garin Allawa, Yusuf Musa, ya shaida wa ƴan jarida cewa ƴan ta'adda sun mamaye kauyen da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadi (Jiya).

Ya bayyana cewa har kawo yanzu ba a tantance yawan mutanen da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su ba.

Maharan sun kona kayan abinci

Ya ce maharan sun kona kimanin shanu 100 da babura 35 da buhunan hatsi iri-iri 150 na mazauna yankin da gidaje 30 yayin wannan mummunan hari.

Mazauna yankin sun koka kan yadda a duk tsawon kilomita ɗaya sai sun ci karo da ‘yan ta’adda, wadanda suka ce suna da sansani na dindindin a dajin Allawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmaki hedikwatar 'yan sanda a Zamfara, bayanai sun fito

Yadda mazauna yankin ke fama da ƴan ta'adda

A makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’umma hari a kauyen da safiyar Juma’a, inda suka kashe wani dan banga tare da yin garkuwa da mutane 12.

Mazauna yankin sun ce bayan harin, ‘yan bindigar sun sake komawa da misalin karfe 9 na daren Juma’a amma jami’an soji suka fatattake su.

An ce harin jiya da daddare ya haifar da tashin hankali, wanda ya tilastawa mazauna garin tserewa zuwa kauyukan Pandogari, Kuta da Gwada.

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sanda da gwamnatin jihar Neja bai cimma nasara ba, Premium Times ta tattaro.

Ƴan bindiga sun sace gawa da ƴan uwa

A wani rahoton kuma Wasu miyagu ɗauke da bindigu sun yi garkuwa da wata gawa tare da masu rakiyarta a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Ƴan bindigan dai sun sace gawar ne lokacin da aka yi jigilarta daga Legas zuwa Nsukka domin binne ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262