Tsadar Rayuwa: Ministan Buhari Ya Goyi Bayan Sarkin Musulmi, Ya Gaya Wa Tinubu Abin da Zai Yi
- An yi kira ga Shugaba Tinubu da ya magance tabarbarewar tattalin arziƙi da ke addabar al’umma
- Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi wannan kiran ne yayin da ya ƙalubalanci manufofin Shugaba Tinubu na tattalin arziki
- Dalung wanda ya goyi bayan matsayin sarakunan Arewa kan tsadar rayuwa a Najeriya, ya shaida wa Tinubu da ya samar da mafita kan halin da ake ciki a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya samar da hanyoyin magance matsalolin tattalin arziƙi da matsalar abinci da ke addabar al’umma.
Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba 14 ga watan Fabrairu, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya tabbatar da cewa Najeriya na zaune a kan bam wanda zai iya tarwatse wa a ko wane lokaci.
Sarkin ya lura cewa ƙasar na kira wa kanta matsala duba da yadda take da ɗimbin matasa marasa aikin yi ba tare da abinci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya kare gwamnatin Tinubu, ya kuma shaida wa Sarkin Musulmi cewa ba za a iya tinkarar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu na rashin tsaro da talauci ba a dare ɗaya.
Me Solomon Dalung ya ce?
Duk da haka, Dalung, a cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, ya gaya wa shugaban ƙasan cewa bai kamata ya. yi watsi da ƙorafin da sarakunan gargajiyar suka gabatar ba.
Tsohon ministan ya rubuta cewa:
"Cikin da babu komai a cikinsa ba ya sauraron muryar bishara", ba za a iya watsi da ƙararrakin damuwa musamman na sarakunan gargajiya ba. Nima na goyi bayansu, @officialABAT yunwa gishirin bala'i ce, shin za ku iya zama a gida kuma ku yi aiki sosai idan hikimarku ba za ta iya samar da mafita ba?
Sarkin Musulmi Ya Bukaci a Koma Ga Allah
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya ba ƴan Najeriya shawara kan hanyar da za su fita daga ƙumcom rayuwar da suke ciki.
Sarkin Musulmin ya yi nuni da cewa hanya mafi dacewa ta fita daga cikin ƙuncin rayuwa ita ce komawa ga Allah wajen yin addu’a.
Asali: Legit.ng