Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Shugaba Tinubu Ya Samu Babban Mukami a Afirika
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya mayar da martani kan sabon muƙamin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu
- A ranar Juma'a, Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU ) ta naɗa Shugaba Tinubu a matsayin zakaran samar da lafiya a Afirika
- Sani ya ce bayan da Super Eagles ta Najeriya ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na AFCON a hannun Ivory Coast, yanzu ƙasar ta zama zakaran lafiya a Afirika
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana sabon matsayin Najeriya a nahiyar Afirika.
Sani ya ce Najeriya yanzu ta zama zakaran lafiya a Afirika bayan Super Eagles ta yi rashin nasara a gasar cin kofin AFCON 2023 a hannun mai masaukin baki, Ivory Coast a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @ShehuSani, a ranar Juma’a, 16 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga muƙamin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).
A kalamansa:
"Mun yi rashin nasara a gasar AFCON a Abidjan amma yanzu mun zama 'Zakarun lafiya' a Afirika."
Ƴan Najeriya sun mayar da martani yayin da Tinubu ya samu sabon muƙami
ŘÊ£ΊŤ@simpleiykejnr
"Lafiya a Afirka! Shugabanmu da ƴan siyasarmu har yanzu suna fita waje don neman lafiya…"
Adams @osagie_adams
"Kar a yi ƙarya, tun da Bulaba yana zuwa Faransa a kodayaushe don duba lafiyarsa, mun cancanci zama a cikin matsayi na ɗaya akan lafiya."
clinton @esiabaclinton1
"Zakaran lafiya yana zuwa Faransa don samun kulawar likitoci. Kun cika wasa a ƙasar nan."
Evergreen @Chris_Okp
"Ɓabu abin da Allah ba zai iya yi ba."
Easy@TadeOmole
Balablue din mu har yanzu yana tafiya a duba lafiyarsa a ƙasar waje, har ma za ka iya samun sirinji a asibitin Aso Villa. Zakaran bala'i.
Afenifere Sun Goyi Bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere ta caccaki masu sukar gwamnatin Tinubu kan halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana cewa masu sukar Tinubu sun yi shiru a lokacin mulkin Buhari wanda shi ne ya jawo halin da ake ciki a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng