Badakalar N72m: ICPC Ta Gurfanar da Tsohon Shugaban ASCSN Bayan Tinubu Ya Dakatar da Shi

Badakalar N72m: ICPC Ta Gurfanar da Tsohon Shugaban ASCSN Bayan Tinubu Ya Dakatar da Shi

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da Bola Audu, tsohon shugaban kungiyar ACSSN bisa zargin almundahana
  • Hukumar na zargin Audu, wanda tsohon ma’aikaci ne a ofishin Akanta Janar na tarayyar Najeriya da laifin karkatar da naira miliyan 72
  • Haka kuma, ana zargin Audu ya karkatar da naira miliyan 3 a zaben kungiyar ACSSN, tuhume-tuhumen da ya musanta gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Auja - A ranar Alhamis ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (ICPC) ta gurfanar da Bola Audu, tsohon babban ma’aikaci a ofishin Akanta Janar na tarayyar Najeriya.

An gurfanar da Audu, gaban Yusuf Halilu, alkalin babbar kotun birnin tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja bisa zargin karkatar da naira miliyan 72.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Gwamnati ta rufe wani babban kanti a Abuja, an samu cikakken bayani

Badakalar N72m: ICPC ta Bola Audu gaban babbar kotun tarayya.
Badakalar N72m: ICPC ta Bola Audu gaban babbar kotun tarayya. Hoto: @icpcnigeria, @akunnachux
Asali: Twitter

A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta dakatar da Audu daga aiki bisa zarginsa da hannu a almundahanar makudan kudaden.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Audu ya musanta tuhume-tuhumen da ake yi sa

Daga baya kuma aka kore shi daga matsayin mamba kuma shugaban kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta Najeriya (ACSSN) bisa zargin yi wa kungiyar zagon kasa.

Mista Audu ya musanta laifuka biyar da ake tuhumarsa da su a lokacin da aka karanta masa laifukan a ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito.

Bayan kin amsa laifin da ya yi, Osuobeni Akponimisingha, mataimakin babban jami’in shari’a a ICPC, ya bukaci a sanya ranar da za a fara shari’ar.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Babatunde Adewusi, ya bukaci kotun da ta ba wanda yake karewa damar beli, bukatar da lauyan da ya shigar da karar bai yi adawa da ita ba.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya janye tuhumar da ake kan dan takarar shugaban kasa da Buhari ya gurfanar

Laifukan almundahana da ake zargin Audu ya aikata

Duk da karbar bukatar belin, alkalin kotun, Mista Halilu ya ce za a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yarin Kuje da ke Abuja idan har ya gaza cika sharuddan belin.

A tuhume-tuhume biyar, gwamnati na zargin Mista Audu da karkatar da naira miliyan 69 da aka fitar domin sayen motar motsa jiki na ofishin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati (ACSSN).

A wata tuhumar kuma, mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa Mista Audu ya karkatar da naira miliyan 3 a zaben kungiyar.

An dage sauraron karar har zuwa ranar 6 ga Mayu domin fara shari'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.