Yadda Buhari Ya Sa Hannu Aka Fitar da Dala Miliyan 10 Don Yin Wani Aiki Bisa Kuskure, Adesina

Yadda Buhari Ya Sa Hannu Aka Fitar da Dala Miliyan 10 Don Yin Wani Aiki Bisa Kuskure, Adesina

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Femi Adesina ya tona yadda wasu mutane suka yaudari Buhari ya saka hannu kan wani aikin iskar gas
  • A cikin littafin aiki da Buhari da ya wallafa, Adesina ya ce tsohon shugaban kasar ya ce a fitar da dala miliyan 10 domin yin aikin bisa kuskure
  • Adesina ya kara da cewa sai daga baya ne Buhari ya gane ya yi kuskure yayin da shugaban kamfanin NBET ya ankarar da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An gano yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu aka fitar da dala biliyan 10 don aikin samar da iskar gas a bisa kuskure.

A cikin wani littafi, an gano yadda kamfanin lantarki na NBET ya samu amincewar Buhari don kai iskar gas wa kamfanin wuta na Neja Delta (NDPH) duk a bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Femi Adesina ya fadi yadda Buhari ya fitar da miliyoyin dala bisa kuskure
Femi Adesina ya fadi yadda Buhari ya fitar da miliyoyin dala don yin wani aiki bisa kuskure. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban Buhari ta fuskar watsa labarai, Femi Adesina ne ya wallafa littafin mai taken 'Aiki tare da Buhari', The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fitar da kudin aikin ne bisa kuskure - Adesina

Littafin ya ruwaito cewa, shugaban kamfanin NBET, Marilyn Amobi da Buhari, sun sanar da cewa shirin PRG na bankin duniya ne ya ba da kudin don gudanar da aikin.

Premium Times ta taba ruwaito cewa an kashe dala miliyan 10 wajen samar da iskar gas ga kamfanin samar da lantarki na Calabar (CGCL) wanda ke karkashin kamfanin NDPH.

Yayin da Amobi aka ruwaito ya nuna adawa da wannan kuduri na fitar da kudin tare da ankarar da shugaban kasar, Buhari ya ce gurguwar shawara aka bashi tun farko.

Buhari na da saurin yarda da mutane - Adesina

Kara karanta wannan

IMF ta fallasa karyar Najeriya, Gwamnati ta dawo da tallafin man fetur da aka cire

Wannan ya jawo masu ruwa da tsaki da dama suka rinƙa zargin ko an sha ba shugaban kasar irin wannan shawarar na fitar da kudi ba tare da sanin abin da za a yi da su ba.

An samu wannan bayanin ne a lokacin da ake zargin wasu sun kwafi sa hannun Buhari wajen fitar da kudade daga bankin CBN yayin da aka ce dillalan iskar gas na bin bashin dala biliyan 1.3.

Littafin ya kuma ruwaito yadda Amobi ya ce Buhari na da saurin yarda da bayanan da aka kai masa ko da ba shi da ilimi akai.

Gwamnatin ta rufe kantin Sahad na Abuja, an gano dalili

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa (FCCPC) ta rufe babban kantin Sahad na Abuja.

Hakan ta biyo bayan yadda aka gano kantin na cajar masu sayayya kudin da suka haura wanda aka rubuta a jikin kayan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel